Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-28 15:54:37    
Wani mutum na zamanin da na kasar Sin mai suna Wang Anshi

cri

Wang Anshi dan siyasa ne kuma mawallafin adabin kasar Sin na karni na 11. Ba a taba ganin himmar da ya yi wajen yin kwaskwarima kan siyasa da tattalin arziki ba, a wajen wallafa littattafan adabi, ya sami sakamako da yawa kuma yana yaduwa daga zuri'a zuwa zuri'ar jama'ar kasar Sin, ya yi tasiri sosai gare su.

An haifi Wang Anshi a shekarar 1021 a wani gidan babban mutum, tun lokacin da yake karami, hazikancin da ya nuna ya fi na sauran mutane. An bayyana cewa, bai taba manta abubuwan da ya taba karantawa ba, in ya soma rubuta bayanai, ya yi ya yi ba tare da tsayawa ba. Sa'anan kuma ya kan je yawo a wurare daban daban na kasar tare da mahaifinsa. Ya taba rubuta wani bayanin da ke da lakabi haka: Bakin ciki da aka yi wa Zhong Yong, bayanin ya bayyana cewa, Wang Anshi ya gamu da wani yaro mai suna Fang Zhongyong wanda halinsa ya yi kama da aljani. A lokacin da ya cika shekaru 5 da haihuwa, ya iya wallafa wakoki masu kyau sosai, shi ya sa mahaifinsa ya yi farin ciki sosai, ya kan shiga aikace-aikace iri iri don samun moriya tare da Fang Zhongyong. Daga baya, dayake ba a ba shi ilmi sosai ba, a kai a kai ne Fang Zhongyong ya zama yaro tamkar yadda sauran yara su ke. Bayanin nan an mayar da shi don shawo kan mutanen bayansa cewa, ya kamata su kara samun ilmi, har ma a yanzu an shigar da bayanin cikin littafin karatu a makarantu.

A lokacin da Wang Anshi ya cika shekaru 20 da haihuwa, ya sami wani mukami. A cikin shekaru fiye da 20 da suka wuce, Wang Anshi ya yi gwajin kwaskwarima a kan abubuwan zamantakewar al'umma ta hanyar hakikanin aikin da ya yi, har ma ya yi godiyar kin karbar mukamin da sarkin ya kara masa sau da yawa, a lokacin da ya amince cewa, ya riga ya kware sosai wajen yin gwajinsa a wurare da yawa, sai ya amsa kirar sarki, kai mukaminsa ya yi ta samun ci gaba. A shekarar 1070, Wang Anshi ya cika shekaru 50 da haihuwa, ya zama waziri, bisa goyon bayan sarki ne, ya soma kwaskwarima bisa babban mataki a duk fadin kasar.


1  2