Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-26 14:10:11    
Bayani game da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet

cri

Game da maganar kiyaye muhalli a tudun Qinghai-Tibet, da karo na farko ne kasar Sin ta kafa tsarin sa ido kan aikin kiyaye muhalli lokacin da ake shimfida hanyar dogo ta Qinghai-Tibet. A yankunan gadun daji da albarkatun da ke cikinsu, an gyara shirin shimfida hanyar dogo sai hanyar dogo ba ta ratsa wadannan yankuna ba. A wasu wuraren da namun daji suke da zama, an kafa hanyoyi 25 da namun daji za su iya ratsawa. Bugu da kari kuma, a kan daidaita lokacin yin wannan aiki domin tabbatar da zaman rayuwar namun daji.

Game da maganar rashin iska mai karfi a kan tudun Qinghai-Tibet, kamfanonin da suka halarci ayyukan shimfida hanyar dogo ta Qinghai-Tibet sun dauki matakai iri iri, ciki har da samar da jakunkuna da akwatuna na iskan Oxygen da gina tasoshin samar da iskan Oxygen ga dukkan mutanen da suke aikin shimfida hanyar dogo ta Qinghai-Tibet. A cikin jiragen kasa na fasinjoji kuma akwai tsarin samar da iskan Oxygen ga fasinjoji.

Tun daga ran 1 ga watan Yuli na shekarar da muke ciki, akwai jiragen kasa guda 4 da za su tafi birnin Lhasa ta hanyar dogo ta Qinghai-Tibet daga birnin Beijing da birnin Chengdu da birnin Shanghai da birnin Guangzhou da birnin Xining. (Sanusi Chen)


1  2  3