A watan Yuli na shekarar 1994, bayan da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya kira taron fadin albarkacin baki game da aikin Tibet, ma'aikatar kula da zirga-zirgar hanyar dogo ta kasar Sin ta fara zaben shirye-shirye iri iri wajen aikin shimfida hanyar dogo a Tibet. Kuma ta bayar da shawarar sake shimfida hanyar dogo da ta hade lardin Qinghai da jihar Tibet mai cin gashin kanta. A watan Fabrairu na shekara ta 2001, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta amince da shirin shimfida hanyar dogo ta Qinghai-Tibet. Nan da nan ne a watan Yuni na wannan shekara, aka fara shimfida sashe na biyu na hanyar dogo ta Qinghai-Tibet.
A cikin ayyukan sashen biyu na wannan hanyar dogo, tsawon hanyar dogo da tsayinta ya kai fiye da mita 4000 daga leburin teku ya kai kilomita 960. Tsayin sashen da ya ratsa bakin tudun Tanggula ya kai mita 5072 daga leburin teku, wato ya fi tsayi a cikin dukkan wannan hanyar dogo. Bugu da kari kuma, halin kasa na yankunan da wannan hanyar dogo take ratsawa yana da wahala sosai. Tsawon yankunan dusar kankara da hanyar dogo take ratsawa ya kai fiye da kilomita 550. Sabo da haka, lokacin da ake shimfida wannan hanyar dogo ta Qinghai-Tibet, an fuskanci batutuwa 3 da suka fi tsanani a duk duniya, wato batun dusar kankara da batun kiyaye muhalli da batun rashin iskan Oxygen.
Ta yadda za a kau da maganar dusar kankara, masu kimiyya da fasaha na kasar Sin sun dauki matakai iri iri. Wato, lokacin da ake shimfida harsashin ginin wannan hanyar dogo, an mai da hankali kan yadda iska za ta iya wucewa kuma da kiyaye zafi a cikin harsashin ginin hanyar. A wasu wuraren da ke da dusar kankara da yawa, an gina wasu gadoji. A kan wadannan gadoji ne aka shimfida hanyar dogo.
1 2 3
|