A kasar Mauritius, an gina hotel ne a bakin teku. Sabo da haka, idan ka bude taga, sai ka ga ruwan teku a ko ina, a karkashin ruwan teku sai rairayi da kumba. A kan hanyar da ke tsakanin hotel da hotel, kana iya ganin itutuwa na wuraren zafi, kana kuma iya ganin manyan duwatsu da samariya da gajimare mai kyaun gani.
A kan rairayi farin fat, kana iya samun hasken rana sosai, kana iya iyo a cikin teku, kana iya kallon kifaye masu launuka daban daban. Idan ka yi sa'a, to, kana iya ganin tsohon jikin jirgin sama da ya nitse cikin teku.
Kana iya zagaya a tsibirin Mauritius da jirgin ruwa mai suna 'Catamaran Cruise', a cikin jirgin ruwan, kana iya kallon magangarar ruwa, a sa'i daya kuma kana iya cin abinci. Jirgin ruwa na 'Catamaran Cruise' zai dauke ka zuwa wani karamin tsibiri mai suna 'Ile aux Cerfs'. Abin da ya fi jawo hankulan 'yan yawon shakatawa na tsibirin shi ne ruwan teku mai haske garau. Ruwan tekun ba mai zurfi ba ne, sabo da haka kana iya iyo a cikin ruwan cikin walwala.
A cikin kasar Mauritius, akwai manyan itatuwa da tuddai da magangarar ruwa da kwari, da kyawawan tabkuna. Ban da wadannan abubuwa kuma, al'adu da abinci da kide-kide masu bambanci sun hadu a kasar Mauritius, to, wannan yana jawo hankulan 'yan yawon shakatawa sosai. Idan ka sami dama, sai ta dandana wani irin abinci musamman mai suna 'DhollPurri', idan ka ci, to, ba za ka manta da shi ba.
1 2 3
|