Kasar Mauritius tana gabashin kasar Madagascar, mutanen wurin suna magana da Turanci da Faransanci da harshen Keliao, yawan asalin Sinawa da ke zama a kasar ya kai kashi 5 daga cikin dari na dukkan mutanenta.
A da Mauritius wani tsibiri ne da babu mutane da yawa a kai. A shekarar 1505, wani 'dan kasar Portugal ya isa wurin, a shekarar 1598, 'yan kasar Holland sun isa tsibirin Mauritius, a shekarar 1715, kasar Faransa ta fara mallakar tsibirin. A shekarar 1810, sojojin kasar Britaniya sun murkushe Faransa, sabo da haka a shekarar 1814 tsibirin Mauritius ya zama wani wuri da 'yan mulkin mallaka na Britaniya ke da iko a kai.
Bayan haka, an dauki bayi da fursunoni da farar hula da yawa daga nahiyar Amurka da ta Afirka da India domin su yi aikin gona a tsibirin Mauritius. A ranar 12 ta watan Maris na shekarar 1968, Mauritius ta samu 'yancin kai, a shekarar 1992, Mauritius ta canza sunanta da ya zama jamhuriyyar kasar Mauritius.
1 2 3
|