Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-31 21:36:22    
Shan taba zai iya kashe mutane

cri

Tare da bunkasuwar kimiyya da fasaha, mutane suna nan suna kara sani yadda shan taba zai iya lahanta lafiyar jikinsu kuma za su iya kamu da ciwon consir, amma yawan mutanen da suka shan taba ba su ragu ba, har suna nan suna karuwa sosai. Shin ina dalilin da ya sa irin halin da ake ciki da ya bullo? An ce akwai dalilai da yawa, na farko; kamfanonin sayar da ganyen taba na kasashe masu arziki sun yi gayyar neman babbar moriya sai sukan kago sabbin ganyen taba da yin farfaganda cewa, a cikin ganyen taba da suka sayar ba su da mugun abu, wato sukan gabatar da sabbin kayayyakin taba, wadannan kayayyakin taba sun iya jawo sha'awar mutane sosai da sosai. Kuma ta hanyoyi daban daban ne suka yi barbaza cewa, a cikin kayayyakin taban da suka sayar akwai abubuwan gina lafiyar jiki kuma masu kamshi kuma tare da Vitamin iri iri.Amma, likitoci sun baya mana cewa, ko ta yaya za a kara abubuwa a cikin kayayyakin taba, dukkansu za su iya lahanta lafiyar jikin mutane. Ta haka ne kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta nemi gwamnatoci na kasashe daban daban da su dauki matakai masu karfi don hana fitar da kayayyakin taba ta kowace hanya.


1  2  3