
Wani labarin da wakilin rediyon kasar Sin dake birnin Geneva ya rubuto mana ya ce, ran 31 ga watan Mayu na shekarar nan da muke ciki, ranar hana shan taba na karo na l9 na duk duniya. Babban batu na ranar hana shan taba na Bana shi ne shan taba zai iya kashe mutane. Kuma kungiyar kiwon lafiya ta duniya tana fatan ta hanyar yin farfaganda kan wannan babban batu za a iya daga matsayin sani na dimbin jama'a, musamman za a sa samarin maza da na mata da yara manyan gobe za su iya kara sani cewa, shan taba zai iya kawo mugun sakamako ga lafiyar jikinsu, ta yadda za su bi hanyar gina lafiyar jikinsu don kago wani kyakkyawan muhalli na zaman rayuwarmu.
Bisa kididdigar da aka yi an ce, yanzu yawan mutanen da suka shan taba a duk duniya sun kai kashi daya cikin kashi shida,Kana kuma yawan mutanen da suka mutu saboda shan taba sun kai miliyan 5 a kowace shekara. Kwararru sun bayyana cewa, in ba a hana fitar da ganyen taba ba,a cikin karnin da muke ciki, yawan mutanen da za su mutu sabo da shan taba za su sami ninki biyu bisa na karnin da ya shige.Bugu da kari kuma mutanen da suka shan taba cikin dogon lokaci sukan iya kamu da ciwon consir na huhu da na makogwaro. Kana kuma matan dake yin zaman rayuwa tare da wadannan mutane masu shan taba sosai su ma za su iya fi kamu da ciwon consir.
1 2 3
|