Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-31 15:26:10    
Shugaban kasar Columbia Alvaro Uribe

cri

Dalilin da ya sa fararren hula masu yawa suka nuna gayon baya gare shi shi ne sabo da ya dauki kwararan mataki ga dakaru masu yin adawa da gwamnatin. Kullum a kan kiransa a matsayin " jarumi na har abada", sabo da bai ji tsoron kome ba dangane da ayyukansa. Haka kuma domin yaki da dakaru masu yin adawa da gwamnatin kasar da kuma masu aikin fasa kwauri na kwayoyi, an taba yin yunkurin hallka shi. A cikin shekara ta 1983, 'yan yakin sunkuru sun yi garkuwa da mahaifin Uribe sa'an nan kashe shi. Ta haka Uribe ya gano cewa, yakin basasa da rikicin nuna karfin tuwo sun kawo wa fararren hula na kasar Columbia wahaloli da yawa, kuma yana da muhimmanci sosai kan mallakar sojojin masu karfi. Sabo da haka bayan da ya zama shugaban kasar, ya dauki kwararan matakai ga dakaru masu yin adawa da gwamnatin a maimakon yin shawarwarin zaman lafiya kawai kamar yadda tsohuwar gwamnatin ta yi a da, a waje daya kuma ya karfafa kai wa dakaru 'yan yakin sunkuru farmaki, ta yadda aka dakusar da kungiyoyin 'yan yakin sunkuru masu yin adawa da gwamantin kasar, bugu da kari kuma ya kwance damarar dakaru masu tsattsauran ra'ayi fiye da dubu 30 ta hanyar yin shawarwari. Ta haka a cikin wa'adin aikinsa na farko, halin zaman lafiya da kasar ke ciki ya samu kyautatuwa kwarai da gaske.

Manufofin da gwamnatin Uribe ta aiwatar sun cimma burin fararren hula na kasar, sabo da haka ta samu goyon baya mai yawa daga fararren hula da jam'iyyun siyasa daban daban na kasar. (Kande Gao)


1  2  3