Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-29 21:22:03    
Kasashen duniya suna yin kokarinsu don taimaka kasar Indonisea saboda bala'in girgizar kasa

cri

Da farko, girgizar kasar ta lalata manyan hanyoyin mota na birnin Yogyakarta, musamman ma hanyar tashar jirgin sama na birnin., wannan ya sa da wuya a sauka da kayayyakin ba da agaji, shi ya sa ana bukatar jirgin sama mai saukar ungulu. Na biyu kuma girgizar kasa ta lalata gidaje da yawa a birnin, sannan babu na'urar haka kasa da sauran na'urorin zamani, wannan ya sa da wuya a ceto mutane wadanda gini ya dannesu. Na uku, saboda akwai mutane da yawa da suka ji rauni, asibitin da ke birnin suan cike da mutune, kuma ana karancin magani sosai, wannan zai sa mutane masu ji rauni su mutu a asibiti. Na hudu, yanzu ana maras abinci da ruwan sha sosai a wurin, wasu mutune sun fara neman abinci a karkashin buraguzan gine gine, kungiyar Red Cross ta kasar Indonesia tana nuna damuwar cewa wannan zai haifar da yaduwar kwayoyin cuta. Na biyar, girgizar kasar ta katse wutalantarki da sadarwa a birnin, mutane ba za su iya samun labarin danginsu ba, hankali ya tashi sosai, kuma wannan ya sa aikin ba da agaji a cikin mawuyacin hali.

Kasar Sin da kasashen Asiya ta kudu maso gabas sun ba da taimakonsu nan da nan. A ranar da girgizar kasa ta faru, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da gudummawar dolar miliyan biyu na Amurka ga Indonisa, kuma za ta ba da taimako bisa halin da ake ciki. Ran 28 ga wata, firayin minista Thaksin Shinawatra na kasar Thailand ya bayar da sanarwa don nuna tausayi ga mutunen kasar Indonesia da suka gamu da bala'in, kuma ya ce kasar Thailand za ta ba da taimako ga kasar Indonesia tare da membobin gammayar kasashen Asiya ta kudu maso gabas.ran 27 ga wata, firayin minista Lee hsien loong na kasar Singapore ya buga waya ga shugaba Susilo Bambang Yudhoyono na kasar Indonesia ya ce, kasar Singapore za ta ba da kayayyakin agaji da darajarsu ta kai dubu 50. A ran 28 ga wata, kasar Singapore ta sake aika da kungiyoyin ba da agaji ga Indonesia. Shugabar Gloria Macapagal Arroyo ta kasar Philippines ta riga ta ba da iznin kafa wata kungiyar agaji zuwa kasar Indonesia. Kasar Malaysia ta riga ta aika da wata kungiyar agaji kunshe da likitoci da masu ba da agaji zuwa wurin, kuma ta aika da abinci da kayayyakin agaji da yawa.


1  2  3