Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-22 18:37:42    
Kasar Sin ta samu ci gaba wajen yin nazari kan ilmin Tibet

cri

Bisa kididdigar da aka yi, yanzu kimanin mutane 2000 ciki har da 'yan kabilar Tibet da 'yan kabilar Han da kabilar Hui da na sauran kananan kabilu na kasar Sin suna nazarin ilmin Tibet. A duk fadin kasar Sin, yawan hukumomin yin nazarin ilmin Tibet da koyar da ilmin Tibet da hukumomin dab'i ya kai gomai.

Lokacin da ake yin amfani da ilmin kabilu da ilimin dan Adam da ilmin zaman al'umma kan aikin yin nazarin ilmin Tibet, masanan kasar Sin suna kuma mai da hankali sosai wajen yin mu'amala da hadin guiwa da takwarorinsu na ketare. A gun taron, Mr. Fernand Meyer, wani dan Faransa ne wanda ya kware sosai kan ilmin Tibet ya iya yaren Tibet sosai. Ya riga ya juya wasu litattafan likitanci na Tibet zuwa Faransanci daga yaren Tibet. Ya kuma yaba wa aikin yin nazarin ilmin Tibet da kasar Sin take yi. Ya ce, "A cikin shekaru 20 ko 30 da suka wuce, kasar Sin ta samu ci gaba sosai wajen yin nazari kan ilmin Tibet. Ina son litattafan da masanan kasar Sin suka rubuta kwarai. Ina ganin cewa, yanzu ya kamata mu yi hadin guiwa a kan wasu fannoni, ba ma kawai a yi musayar wasu labaru ba."

Dr. Geleg, wani masani na cibiyar yin nazari kan ilmin Tibet ta kasar Sin wanda zai yi hadin guiwa da Mr. Meyer kan ilmin Tibet, ya ce, ya zuwa yanzu, masana fiye da 120 na cibiyar yin nazari kan ilmin Tibet sun riga sun ziyarci kasashe da yankuna fiye da 40, kuma sun yi ta yin mu'amala da takwarorinsu na kasashen waje. A sa'i daya kuma, masana fiye da dari 3 sun kawo wa kasar Sin ziyara, kuma sun juya tare da wallafa litattafai da yawa da suke shafar ilmin Tibet daga yaren Tibet zuwa harsunan kasashensu. Mr. Geleg ya ce, "Ta irin wannan musanye-musanyen da aka yi a tsakaninmu, za mu iya koyon hanyoyi da matakai na zamani wajen yin nazari, kuma za a iya kyautata halin da muke ciki wajen yin nazari. Bugu da kari kuma za mu iya bayyana wa kasashen waje sakamakon da muka samu wajen yin nazarin ilmin Tibet. "

Mr. Tsewang Jigme, shugaban cibiyar ilmin kimiyya na zaman al'ummar Tibet, wato wata hukumar ilmin Tibet, ya ce, lokacin da ake yin nazari kan al'adu na Tibet, ana kuma yin nazarin ilmin Tibet bisa halin da ake ciki a jihar Tibet ta yanzu domin ba da hidima ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar Tibet. (Sanusi Chen)


1  2