Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-22 18:37:42    
Kasar Sin ta samu ci gaba wajen yin nazari kan ilmin Tibet

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barka da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Mu leka kasar Sin. A kwanan baya, masana fiye da dari 2 wadanda suke nazarin ilmin Tibet sun yi taro a nan birnin Beijing domin taya murnar cikon shekaru 20 da kafuwar cibiyar yin nazarin ilmin Tibet ta kasar Sin. A gun taron, masana sun bayyana cewa, yanzu aikin yin nazari kan ilmin Tibet ya samu ci gaba cikin sauri sosai. yanzu ga wani bayanin da wakiliyarmu ta aiko mana.

Ilmin Tibet ilmi ne game da tarihi da zaman al'umma da al'adu na kabilar Tibet. Ana nazarin zaman al'umma da tarihi da siyasa da tattalin arziki da addini da adabi da kide-kide da wakoki da wasannin kwaikwayo da gine-gine da magunguna da dai sauransu na kabilar Tibet. A farkon karni na 19 da ya gabata, masanan kasashen yammacin duniya sun fara mai da hankali kan al'adun kabilar Tibet. A shekarar 1823, Alexander Csoma de Koros, wani masanin kasar Hungariya ya fara koyon yaren Tibet, kuma ya fara yin nazari kan al'adu da tarihin kabilar Tibet. Shi ne ya kirkiro kalmar "Ilmin Tibet". A karni na 20 da ya gabata, aikin yin nazari kan ilimin Tibet ya samu bunkasuwa sosai a kasashen Britaniya da Faransa da Amurka. Sabo da haka, ilmin Tibet ya fara zama wani ilmin da ke shafar kasashen duniya a kai a kai.

Kasar Sin gari ne na ilmin Tibet. Ko da yake ba da dadewa ba ne aka fara yin nazari kan ilmin Tibet, amma ya samu ci gaba kwarai. Lhakpa Phuntsok, babban direktan cibiyar yin nazari kan ilmin Tibet ta kasar Sin ya bayyana cewa: "Ya zuwa yanzu kasar Sin ta riga ta kafa wani cikakken tsarin ilmin Tibet da ke shafar fannoni daban-dabam. An kuma sami sakamako da yawa kan wannan aiki. Wasu masana samari da masana wadanda suke da matsakaitan shekarun haihuwa sun zama muhimmin karfi wajen nazarin ilmin Tibet."

1  2