Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-18 21:03:39    
Hukumomin binciken sauye-sauyen yanayin sararin sama na  Sin suna kokarin bauta wa jama'a

cri

A hakika dai, mutanen Sin masu dimbin yawa suna mai da hankali ga labarun sauye-sauyen yanayin sararin sama da ake bayarwa, ba ma kawai domin za su san sauye-sauyen yanayin sararin sama ba, musamman domin a kan gamu da bala'in yanayin a kasar Sin, kamar mahaukaciyar guguwa da ruwan sama mai karfi da ambaliyar ruwa da sauran irinsu. Sabo da haka bayar da labarun yanayin sararin sama daidai kuma cikin lokaci yana taka muhimmiyar rawa wajen ba da tabbaci ga bunkasa tattalin arzikin kasa da zaman jama'arta da kare dukiyoyin jama'a da rayukansu.

Malam Qin Dahe, shugaban hukumar binciken sauye-sauyen yanayin sararin sama ta kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu, kasar Sin ta riga ta kafa kwarya-kwaryar tsarin binciken yanayin sararin sama daga duk fannoni don bayar da labarun yanayin sararin sama ga jama'a daidai kuma cikin lokaci. Ya ce, "a cikin shekarun nan biyar da suka wuce, hukumar binciken sauye-sauyen yanayin sararin sama ta kasar Sin ta sami injunan Radar na zamani sama da 100, ta kafa tashoshin binciken sauye-sauyen yanayin sararin sama masu aiki da kansu wadanda yawansu ya zarce 7500, kuma ta sayi naurori masu aiki da kwakwalwa na zamani. Haka nan kuma an fara aiki da taurarin bil-adam masu lambar Fengyun C da D domin binciken sauye-sauyen yanayin sararin sama."


1  2  3