
Ran 18 ga wata, an yi taron kimiyya da fasaha a kan yanayin sararin sama na kasar Sin a birnin Beijing. Jami'an hukumomin binciken sauye-sauyen yanayin sararin sama na kasar Sin wadanda suka halarci taron sun bayyana cewa, yanzu, kasar Sin tana kokarin kafa tsarin bayar da labaru a kan sauye-sauyen sararin sama na zamani.
Malam Chen Guo, dan birnin Beijing ya kan tuka mota a tsakanin gidansa da kuma kamfani da yake aiki. Ya bayyana cewa, duk lokacin da zai yi shirin wanke motarsa, ya kan saurari shawara da hukumar binciken sauye-sauyen yanayin sararin sama ta birnin Beijing ta gabatar. Ya ce, "a nan birnin Beijing a kan samu sauye-sauyen yanayin sararin sama, don haka a duk lokacin da zan wanke motata, tabbas ne, na saurari shawara da hukumar binciken sauye-sauyen yanayin sararin sama ta gabatar, ta yadda na san ko za a yi ruwan sama ko dusar kankara ko kuma babbar iska mai dauke da kura, ko a'a. Bayan haka zan yanke shawara a kan shirina na wanke motata."
1 2 3
|