Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-17 20:02:52    
M.D.D. ta yi shirin aike da rundunar kiyaye zaman lafiya zuwa shiyyar Darfur

cri

Amma har ila yau gwamnatin Sudan tana nuna kiyayya ga jibge rundunar kasashen duniya a shiyyar Darfur. A ganinta kuwa yarda da jibge sojojin M.D.D. a shiyyar zai lahanta mallakan kan kasar Sudan. Amma gwamnatin Sudan ba ta nuna kiyayya ga yin shawarwari da hadin gwiwa a tsakaninta da M.D.D. ba. Sabo da haka cikin kurin da kwamitin sulhu na M.D.D. ya tsayar a ran 16 ga wata ya kirayi sassa daban-daban da abin ya shafa da su ba da taimako ga kara saurin aike da rundunar kiyaye zaman lafiya ta majalisar don maye gurbin rundunar kawancen Afirka. Kasashen Sin da Rasha da Katar kuma sun bayyana cewa, ya kamata M.D.D. ta samu yarda da hadin gwiwa daga wajen gwamnatin Sudan a lokacin da take yin aikin kiyaye zaman lafiya.

A ran 5 ga wannan wata a birnin Abuja, hedkwatar kasar Nijeriya, gwamnatin Sudan da muhimmiyar kungiyar dakaru masu yin adawa da gwamnatin wato "kungiyar neman 'yancin Sudan" sun daddale yarjejniyar shimfida zaman lafiya a tsakaninsu, amma har ila yau rukunin Abdel Wahid Mohammed al-Nur na wannan kungiyar ta ki yarda da sa hannu kan yarjejeniyar. A ran 16 ga wata kwamitin sulhu na M.D.D. ya tsai da kuduri dangane da wannan cewa, zai dauki tsaurarran matakai kan mutane masu zaman kansu da kungiya-kungiya wadanda suke bakin nufin tauye yarjejeniyar zaman lafiya ta Abuja. A wannan rana kuma majalisar zaman lafiya da kwanciyar hankali ta kawancen Afirka ita ma ta bayar da wata sanarwa wadda a ciki ta sa kaimi ga wadannan kungiyoyin dakaru masu yin adawa da gwamnatin kasar da su rattaba hannu a yarjajeniyar zaman lafiya tun kafin ran 31 ga wannan wata.

Manazarta sun bayyana cewa, tsatsauran ra'ayin da M.D.D. da kawancen kasashen Afirka suka nuna wa dakaru masu yin adawa da gwamnati wadanda suke nuna kiyayya ga rattaba hannu kan yarjejeniyar shimfida zaman lafiya, wannan ya nuna niyyar kasashen duniya domin daidaita matsalar Darfur. Amma aike da rundunar kiyaye zaman lafiya na M.D.D. zuwa shiyyar Darfur yana da amfani ga kara kyautata halin kwanciyar hankali mai dorewa na wannna shiyya, da daidaita matsalar samar kayan jin kai. Abin da ya kamata kasashen duniya su yi yanzu shi ne kara yin shawarwari da gwamnatin kasar Sudan, da kara ba da taimako ga tafiyar da yarjejeniyar zaman lafiya ta yadda za a samu tabbaci ga daidaita matsalar Darfur cikin lumana. (Umaru)


1  2