Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-17 20:02:52    
M.D.D. ta yi shirin aike da rundunar kiyaye zaman lafiya zuwa shiyyar Darfur

cri

A ran 16 ga wata kwamitin sulhu na M.D.D. ya zartas da wani kuduri don kara kokarin aike da wata rundunar kiyaye zaman lafiya na majalisar zuwa shiyyar Darfur da ke kasar Sudan. Kudurin kuma ya bayyana cewa, cikin mako mai zuwa za a aike da wata hadaddiyar kungiyar kimantawa a fannin fasaha a tsakanin kawancen kasashen Afirka da M.D.D. zuwa shiyyar Darfur ta kasar Sudan don share fage ga yin aikin kiyaye zaman lafiya.

Shiyyar Darfur tana yammacin kasar Sudan. A watan Fabrairu na shekarar 2003, "kungiyar neman 'yancin Sudan" da "kungiyar gaskiya da adalci" da mazauna bakaken fata na wurin suka kafa sun yi aikace-aikacen yin adawa da gwamnatin kasar. Bisa daidaituwar da kasashen duniya wadanda kawancen Afirka ke yi musu ginshiki, gwamnatin Sudan da dakaru masu yin adawa da gwamnati sun daddale yarjejeniyar tsakaita bude wuta a tsakaninsu a watan Afril na shekarar 2004. A watan Agusta na wannan shekara kuma rundunar sojoji ta kashi na farko da kawancen Afirka ya aika da ita ta sauka shiyyar Darfur don sa ido kan aikin tsakaita bude wuta.

Amma sabo da karancin kudi da kayayyaki, shi ya sa rundunar kiyaye zaman lafiya da ke Darfur tana cikin halin kaka-ni-ka-ni, mutane masu ba da gudummawa na kasashen duniya su ma sun janye jikinsu daga wurin sabo da rashin kwanciyar hankali, ta yadda halin da ake ciki a shiyyar Darfur ta kara tsanani wajen kwanciyar hankali da akidar jin kai. Sabo da haka, M.D.D. ta kara mai da hankali kan wannan shiyya kuma ta fara shirin jibge sojojin kiyaye zaman lafiya a shiyyar.


1  2