Gwamnatin kasar Sinta gabatar da sabon tsarin kirkire-kirkire, wannan ba kawai a wajen kimiyya da fasaha ba ,
har ma a wajen masana'antun al'adu . Yalwatuwar masana'antun al'adu na Lardin Hubei ta sa mutane suka sauya tsohon tunani kuma ta kawo karfin kirkire-kirkire . Alal misali , Kamfanin Jiangtong ya riga ya zama madugu a wajen wallafa sababbin wasannin cartoon a duniya . Amma duk da haka , Mr. Zhu , babban manajan kamfanin ya ce, na gaba za su mai da hankali kwarai a kan ingancin wasannin cartoon . Sa'an nan kuma za su bude kasuwar sayar da wasannin masu ikon mallakar ilmi .
To, jama'a masu karatun shafinmu , shirin "Duniya ina labari " da za mu iya kawo muku ke nan a yau . Ado ne ya fasara wannan bayanin . Da haka muke muku sallama tare da fatan alheri . (Ado ) 1 2
|