Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , a cikin 'yan shekarun da suka shige , a nan kasar Sin tana mai da hankali sosai kan masana'antun al'adu . Gwamnatocin matakai daban daban suna mai da muhimmanci a kansu . Jama'a na bangarori daban daban suna shiga cikin wannan aikin masana'antun . Yanzu larduna da jihohi na kashi 2 cikin 3 na duk kasar Sin sun gabatar da cewar za su kafa masana'antun al'adu da ya zama babbar masana'antarsu . A cikin shirinmu na yau za mu kai ku zuwa Lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin don binciken abubuwan gaskiya a wajen yalwata masana'antun al'adu .
A cikin wani babban gini mai benaye fiye da 10 dake cibiyar birnin Wuhan , hedkwatar Lardin Hubei , kamfanin cartoon na Jiangtun yana mamaye benaye 3 . Wannan kamfanin an kafa shi ne a shekarar 2000 . Kuma ya riga ya zama daya daga cikin kamfanoni masu karfi . Yanzu wannan kamfanin ya riga ya wallafa wasannin kwaikwayon cartoon masu yawa . Mr. Zhu Yougan , babban manajan kamfanin ya ce ,
Tun daga farkon wannan shekara an sayar da wasannin cartoon guda 19 ciki har da " Dodon dake birane " da " Al'ajabi mai shan jini " da sauransu . A watan Nuwamba da ya shige , gabobi biyu na Tekun Zirin Taiwan sun hada kansu sun buga cartoon labarin tarihi mai suna "Sabuwar Daular Song " a sa'I daya . A shekarar 2005 , wasannin cartoon da Kamfanin Jiangtong ya wallafa sun yaye a kudu maso arewacin kasar Asiya . An kiyasta cewa , ya zuwa karshen wannan shekara yawan wasannin katoon zai kai kusan 100 . Wannan ba a iya ganin saurinsu ba a cikin shekaru biyu da suka wuce . Ma iya cewa , bayan da aka fitar da labarun soyayya a hanyoyin sadarwar internet , wasannin kwaikwayon cartoon sun zama sabon salo mai jawo hankulan mutane.
1 2
|