Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-24 21:37:47    
Kasar Sin tana taimakawa yaran kauyuka da suke karatu ba tare da biyan kudi da yawa ba

cri

Yaran kasar Sin suna karatu a makarantun firamare da midil ba tare da biya kudi ba, amma suna bukatar biyan kudaden makaranta da littattafai da dai sauransu, wadannan kudade sun zama babban nauyi ne ga wasu iyalan manoma, saboda haka, wasu yara sun bar makarantu saboda rashin isasshen kudi.

A shekarun nan da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta gane cewa, ba da ilmi a duk fadin kasar yana da muhimmanci soai wajen daga ingancin mutane da kuma mayar da matsin lambar da yawan mutane ya kawo da ya zama albarkatun kasar, shi ya sa ta kara zuba kudi kan ba da ilmin sannu a hankali, ta kuma dauki matakai daban daban don kara karfin raya aikin ba da ilmi na tilas a kauyuka.

Ministan ilmi na kasar Sin Mr. Zhou Ji ya bayyana cewa 'a cikin shirin raya kasa na shekaru biyar biyar na karo na 10 da kasar Sin ta tsara, ta dora muhimmanci sosai kan aikin ba da ilmi a kauyka, a matsayin muhimmancin tsare-tsare. Ta aiwatar da muhimmiyar manufa ta kara zuba kudi kan ba da ilmi a kauyukanta, sa'an nan kuma, ta mai da hankali kan tafiyar da manyan ayyuka da shirye-shirye a jere, ta haka, an dora muhimmanci da kuma kara karfin aikin ba da ilmi a kauyuka kwarai da gaske.'

A kauyukan da ke tsakiya da yammacin kasar Sin, yafe wa dukan 'yan makarantun firamare da midil kudin makaranta da na littattafai, da kuma ba da alawas ga wadanda suke zaune a makarantu muhimman matakai ne da kasar Sin ta dauka a fannin aikin ba da ilmi a kauyuka a shekarun nan da suka wuce.

Tun daga shekarar 2004 har zuwa yanzu, gwamnatin kasar Sin ta ware kudin musamman a ko wace shekara wajen gina dakunan kwana masu tsabta ga 'yan makarantun da suke zama a makarantu. Ban da wannan kuma, kasar Sin ta dauki matakai daban daban don rage gibin da ke tsakanin birane da kauyuka a fannin aikin ba da ilmi.

Don rage wannan gibi, a kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta sake dora muhimmanci kan aikin ba da ilmi a kauyukanta a cikin shirin raya kasa na shekaru 5 masu zuwa. Firaministan kasar Mr. Wen Jiabao ya gabatar da cewa, za ta kara zuba kudi kan aikin ba da ilmi sosai, da kyautata halin da karkara suke ciki a wannan fannin. Ya ce, 'a cikin shekaru 5 masu zuwa, gwamnatin kasar ta kara zuba kudi kan aikin ba da ilmi na tilas da jimlarsa ta kai kudin Sin yuan biliyan 218.2 gaba daya, za ta daga matsayin tabbatar da yin amfani da kudin musamman kan aikin ba da ilmi na tilas a makarantun firamare da midil na kauyuka, da kuma kafa tsarin zuba kudi kan yin kwaskwarima da kyautata dakunan makarantun firamare da midil, ta yadda ko wace yara za su iya samun ilmi na tilas cikin adalci.'


1  2