Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-24 21:37:47    
Kasar Sin tana taimakawa yaran kauyuka da suke karatu ba tare da biyan kudi da yawa ba

cri

Bayan da ya ziyaraci makaratun firamare da midil na garin Zhaojiazhen na lardin Sichuan da ke yammacin kasar Sin. Kan bayanin nan shi ne 'kasar Sin tana taimakawa yaran kauyuka da suke karatu ba tare da biyan kudi da yawa ba'.

A watan Maris na shekarar da muke ciki, makarantun firamare da midil na garin Zhaojiazhen sun fara aiki bi da bi. Iyaye sun shirya wa yaransu kudi, amma abin mamaki shi ne, ba su bukatar biyan kudin makaranta tun daga wannan zangon karatu ba, ta haka, an rage kudin karatu kudin Sin yuan gomai. Wannan ya faranta wa iyayen rai sosai.

'na ji farin ciki sosai, saboda ba zan biya kudi da yawa ba, an rage nauyin da aka danka mini. Ina da 'ya'ya 3, wani yana karatu a makarantar sakantare, wani a makarantar firamare, wani kuma a makarantar midil, a ganina, ban iya jure kudin makaranta da yawa ba.'

Wannan sabuwar manufar da ta faranta wa iyaye rai gwamnatin kasar Sin ne ta gabatar da ita a karshen shekarar da ta gabata. Wato a shekarar da muke ciki, tun daga sabon zangon karatu, an yafe wa 'yan makarantar da suke samun ilmi na tilas a kauyukan yammacin kasar dukan kudin makaranta, sa'an nan kuma, a shekarar mai zuwa za a aiwatar da wannan manufa a kauyukan tsakiya da gabashin kasar Sin, ta yadda za a tabbatar da yafe wa yara fiye da miliyan dari 1 da ke zama a kauyuka dukan kudaden makaranta.

1  2