Musulunci addini ne da ake bi a Saudiyya, kuma bisa Alkur'ani mai girma da kuma Hadisai na annabi Mohammed ne ake aiwatar da dokokin kasar. A Saudiyya, sarki shi ne shugaban kasar, wanda kuma ke da ikon koli a wajen gudanar da harkokin mulki da kuma shari'a.
Saudiyya ta amsa sunanta sosai, wato kasa ta man fetur. Yawan man fetur da ake da shi a kasar da kuma yawan man fetur da take fitarwa duka sun zo na daya a duniya. Man fetur da masana'antar harhada sinadaran man fetur su ne muhimman ginshikan tattalin arzikin kasar. A halin yanzu dai, yawan man fetur da aka gano a Saudiyya ya kai garwa biliyan 261.2, wanda ya dau kashi 26% na yawan man fetur da duk duniya ke da shi. Saudiyya tana fitar da man fetur da nauyinsa ya kai ton miliyan 400 zuwa miliyan 500 a ko wace shekara, bayan haka kuma, tana fitar da kayayyakin man fetur zuwa kasashe da shiyyoyi sama da 70. Yawan kudin da aka samu daga man fetur ya kai kashi sama da 70% na kudin shiga na kasar, kuma yawan man fetur da take fitarwa ya dau kashi fiye da 90% na dukan kayayyakin da take fitarwa. Ban da wannan, Saudiyya ita kuma kasa ce da ke da arzikin iskar gas mai yawan gaske.
A cikin 'yan shekarun nan, Saudiyya ta yi kokarin bunkasa tattalin arzikinta a fannoni daban daban, tana kokarin bunkasa aikin hakan ma'adinai da kananan masana'antu da aikin noma da dai sauransu wadanda ba na masana'antar man fetur ba, don neman gyaran tsarin tattalin arzikinta na dogara bisa man fetur kawai.
Sin da Saudiyya sun dade suna abuta da juna. Tuni a karni na 7, mabiya addinin musulunci sai suka yi doguwar tafiya suka ketare teku har zuwa nan kasar Sin don yada musulunci. A karni na 15 kuma, mashahurin mai jirgin nan mai suna Zheng He shi ma ya taba zuwa Saudiyya. Tun bayan da aka kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Saudiyya a shekara ta 1990, huldar aminci da hadin gwiwa da ke tsakaninsu sai ta yi ta bunkasa lami lafiya, fannonin da aka aiwatar da hadin gwiwa ma sun yi ta habaka. (Lubabatu Lei) 1 2
|