Kasar Saudiyya tana zirin Larabawa da ke kudu maso yammacin Asiya, kuma tana fuskantar tekun Farisa a gabas da kuma dab da bahar Maliya a yamma. Bayan haka kuma, tana iyaka da kasashen Jordan da Iraki da Kuwait da hadaddiyar daular Larabawa da Oman da kuma Yemen. A cikin Larabci, kalmar Saudiyya tana nufin hamada mai farin ciki. Fadin kasar Saudiyya ya kai murabba'in kilomita miliyan biyu da dubu 250, kuma rabin filayen kasar hamada ce. A yankin kasar, babu koguna ko tafkunan da za a iya samun ruwa a ciki a duk shekara. Ana zafi sosai a kasar. Yawan mutanen Saudiyya ya kai miliyan 22 da dubu 670, kuma yawan mutanen birnin Riyadh, wato hedkwatar kasar, ya kai miliyan 4.
Saudiyya ita kuma kasa ce da aka samu mafarin addinin musulunci. A karni na bakwai, mabiya bayan Annabi Mohammadu S.A.W, wato wanda ya yada addinin musulunci, sun kafa daular Larabawa. Daular ta yi ta bunkasa har ma ta fi kasaita a karni na 8, har ma a lokacin filayen daular sun ketare nahiyoyin Turai da Asiya da kuma Afirka duka. Ya zuwa karni na 16, daular Ottoman ta kafa mulki a daular nan. Daga baya, a karni na 19, Birtaniya ta kutsa kai cikin kasar, kuma ta karkasa kasar cikin kashi biyu, wato yankin Hijaz da na Najd. Ya zuwa shekara ta 1924, sarkin yankin Najd ya hada Najd da Hijaz, sakamakon hakan kuma, an fara samun dinkuwar kasar sannu a hankali. A watan Satumba na shekara ta 1932 kuma, an shelanta kafuwar daular Saudiyya.
Birnin Makka, wato birni ne da aka haifi annabi Mohammadu S.A.W, wuri ne mai tsarki ne na farko na addinin musulunci, wanda kuma ake kiransa 'birnin birane'. A ko wace shekara, musulmi miliyoyi daga wurare daban daban na duk duniya su kan je birnin Makka domin yin aikin hajji. Birnin Makka yana kasancewa a yankunan tsaunuka da ke yammacin Saudiyya, kuma fadinsa ya kai kusan muraba'in kilomita 30, yawan mutanensa kuma ya kai kimanin dubu 400.
1 2
|