A cikin babban zaben da aka yi a ran 28 ga watan Maris na shekarar da muke ciki, jam'iyyar Kadima da Olmert ke shugabanta ta samu kujeru 29 daga cikin kujeru 120 na majalisar da za a kafa mai zuwa, a sakamakon haka, jam'iyyar ta zama babbar jam'iyya ta farko, kuma ta samu ikon kafa majalisar dokokin kasar. Olmert ya bayyana cewa, kasar Isra'ila tana cikin shirin raba wasu wurare da kuma janye matsugunan yahudawa daga wuraren nan. Amma a sa'i daya kuma ya jaddada cewa, dole ne a daddale yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Palesdinu da Isra'ila ta hanyar yin shawarwari bisa sharudda biyu, wato aiwatar da taswirar hanyar shimfida zaman lafiya a gabas ta tsakiya da kuma daina yin harkokin nuna karfin tuwo tsakanin kasashen biyu.(Kande Gao) 1 2 3
|