A ran 11 ga wata, majalisar ministocin kasar Isra'ila ta bayar da sanarwar cewa, firayim ministan kasar Sharon ba zai gudanar da aikinsa ba a nan gaba, a sa'i daya kuma ta nada makaddashin firayim minsitan kasar Ehud Olmert da ya zama firayim ministan wucin gadi na kasar.
An haifi Olmert a shekara ta 1945 a wani wurin da ke arewacin kasar Isra'ila. Ya taba karatu a cikin jami'ar Hebrew ta Kudus, daya bayan daya ne ya samu digiri na farko kan ilmin halin dan Adam da na falsafa da kuma na shari'a. Ban da wannan kuma ya taba zama manema labarai, kuma kafin ya sa hannu a cikin harkokin siyasa, shi wani lauya ne.
1 2 3
|