Dangantakar tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin bangarorin nan biyu ita ce daya daga muhimman batutuwa na taron koli na kasashen Sin da Amurka?kullum samu moriyar juna ya kasance amkar ginshikin dangantakar tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka. A cikin 'yan kwanakin da suka wuce, Mr. Bush, shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa:"dangantakar da ke tsakanin kasashen Amurka da Sin tana da yakini, da kuma yamutsi sosai. Ziyarar da Mr. Hu Jintao zai yi tana da muhimmanci sosai. Ya kasance da ratar ciniki da yawan kudinta ya zarce dolla biliyan 200 a tsakanin kasashen Amurka da Sin, ina fata Mr. Hu Jintao zai iya bayyana nufinsa kan matsalar yawan kudin musaya na RMB."
Shekarar nan shekara ce ta cika shekaru 50 da kasar Sin ta kulla huldar jakadanci da kasashen Larabawa da na Afrika. Shugaba Hu Jintao ya kai ziyara ga kasar Saudi Arabia, wannan dai muhimmiyar manufar harkokin waje ce ta kasar Sin wajen kara dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Larabawa. Ra'ayoyin bainal jama'a sun bayyana cewa, shekarar nan "shekarar Afrika" ce ta kasar Sin. Kasashen Morocco, da Nijerya, da kuma Kenya suna arewaci, da yammaci, da kuma gabashin babban yankin Afrika dai-dai, sabo da haka, ana iya ganin cewa, wannan ziyara wani aikin harkokin waje ne da kasar Sin ta yi kan duk nahiyar Afrika. (Bilkisu) 1 2 3
|