Matsalar Taiwan, matsala ce da ta fi muhimmanci da mai jawo hankulan mutane a cikin dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka. Kan matsalar nan, Mr. He Yafei, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin ya ce:"A ganina, tabbas ne bangarorin nan biyu za su yi tattauinawa kan matsalar Taiwan, sabo da ita ce matsala mai muhimmanci sosai a cikin dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka, sau da yawa shugaba Bush, da gwamnatin kasar Amurka sun sake nanata cewa, su tsaya kan manufar kasar Sin daya tak, da kuma tsaya kan hadaddiyar sanarwa 3 ta kasashen Sin da Amurka, da adawa da "neman yancin kan Taiwan". Mu bayyana imani cewa, bangaren Amurka zai ci gaba da jadadda matsayinsa a kan wannan."
1 2 3
|