Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-18 16:51:30    
Gandun kiwon damisoshi na birnin Harbin na kasar Sin

cri

Yanzu, yawan masu yawon shakatawa da ake iya karba a wannan gandu ya kai darurruka a ko wace rana. A cikin gandun nan, wakilanmu sun tarar da wata 'yar yawon shakatawa mai suna Jiang Shu wadda ta fito daga birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin. Ta gaya wa wakilanmu cewa, "irin wannan damisa da ke zama a arewa maso gabashin kasar Sin suna dab da karewa a doron duniya. Sabo da haka suna da daraja kwarai. Gandun nan mai girma ne sosai. Dazu, mun ga irin hanyar da ake bi wajen kiwonsu bakon abu ne gare ni, kuma ya yi kwaikwayon yadda damisoshi ke zama a dazuzzuka. Mu masu yawon shakatawa muna sha'awarta ainun. Mai yiwuwa ne, a karo na farko masu yawon shakatawa suka sami damar kallon wannan. "

Bisa kimantarwa da 'yan kimiyya suka yi, an ce, yawan damisoshi irin na kasar Sin wadanda ke zama a dazuzzuwa bai wuce 500 a duniyar yanzu ba. Babban manajan wannan gandu Malam Wang Ligang ya bayyana wa wakilanmu cewa, makasudin kafa gandunmu shi ne domin gudanar da harkokin yawon shakatawa, kuma musamman domin mayar wa damisoshi rayuwar daji. (Halilu)


1  2  3