Damisa yana daya daga cikin dabobbi da ke dab da karewa da sauri a doron duniya. Irin damisa da ke zama a manyan duwatsu na Xingan da Changbai a arewa maso gabashin kasar Sin suna da girman jiki da kwarjini da kuma kyakkyawan gashi mai walkiya, idan an kwatanta shi da sauran ire-iren damisoshi na duniya, sai a ce, shi sarkin damisa ne.
An gina gandun kiwon irin wannan damisa na kasar Sin ne a karkarar arewacin birnin Harbin na lardin Heilongjiang da ke a arewa maso gabashin kasar Sin. Yawan damisoshi da ake kiwo a wannan gandu ya zarce arbamiyya, gandun nan kuwa gandun kiwon damisoshi ne mafi girma a duniya. A safiyar wata rana ta farkon yanayin bazara, wakilanmu sun tashi daga birnin Harbin, bayan da suka yi doguwar tafiya, sun isa wannan gandun kiwon damisoshi. Fadin gandun nan ya kai kimanin kadada uku. A nan ne suka ga damisoshi da yawa da ke yawo a cikin dazuzzuwa ko bakin kwari da ruwa ya daskare, wasunsu kuma suna karya kumallo cikin hasken rana.
1 2 3
|