Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-17 17:22:26    
Injin wanke tufafi da ke aiki ba tare da yin amfani da garin sabulu ba

cri

Saboda amfanin irin wannan inji yana da kyau, gwamnatin kasar Sin ta ba da lambar yabo ta ci gaban kimiyya da fasaha ga wannan injin musamman a farkon wannan shekara, ta haka, ya zama kaya mai aiki da lantarki kurum ne da ya sami wannan lambar yabo. Tun bayan da aka fara sayar da injin nan a shekarar da ta gabata har zuwa yanzu, masu kashe kudi sun amince da shi sosai.

Darektan harkokin sayarwa na wata babbar kasuwar kayayyaki masu aiki da lantarki da ke Beijing Mr. Ren Zhenhua ya gabatar da cewa, a cikin dukan injunan wanke tufafi iri fiye da 20 na kamfanin Haier da ake sayarwa a kasuwar nan, yawan injin wanke tufafi da ke aiki ba tare da yin amfani da garin sabulu ba da ake sayarwa ya kai fiye da kashi 20 cikin dari.

'ana sayar da irin wannan injin wanke tufafi lami lafiya. Masu ciki sun fi son sayen wannan injin wanke tufafi, saboda sun yi la'akari da jariransu na nan gaba. Idan ba a tsabtaci tufafin jarirai sosai ba, to, wannan ba zai dace da fatan jarirai ba. Yin amfanin da wannan injin wanke tufafi na musamman ya iya kawar da irin wannan damuwa.'

A cikin wannan kasuwa, bayan da ya saurari bayanin da aka yi masa kan wannan injin musamman, kuma ya yi kallon yadda aka yi amfani da shi, Mr. Yang Qinglin ya yanke shawarar sayen wannan injin wanke tufafi na musamman.

'a ganina, sayen wannan injin musamman ya iya yin tsimin kudin garin sabulu, haka kuma, ya amfana wa kiyaye muhalli na kasarmu.'

Saboda injin wanke tufafi da ke aiki ba tare da yin amfani da garin sabulu ba wani kaya ne na zamani, shi ya sa, an ba da babban tasiri kan ra'ayin gargajiya da mutane suke rike. Amma a sakamakon furofagandar da kamfanin Haier ya yi ta yi, kuma ana ya da ilmin zamani a kasar, yanzu mutane sun fara fahimta da amince da tsabtaci tufafi amma ba tare da yin amfani da garin sabulu ba.

Ko da yake wannan injin musamman yana da tsada kadan, farashinsa ya kai kudin Sin yuan dubu 5 ko fiye, amma wasu mutane suna ganin cewa, idan an yi amfani da injin wanke tufafi da ke aiki ba tare da yin amfani da garin sabulu ba, za a iya yin tsimin kudin garin sabulu, in babu garin sabulu, ba a bukatar ruwa da yawa, ta yadda za a yi tsimin ruwa da lantarki. Sabada haka, ko da yake injin wanke tufafi da ke aiki ba tare da yin amfani da garin sabulu ba yana da tsada, amma a galibi dai, an yi tsimin kudi.

Injin wanke tufafi da ke aiki ba tare da yin amfani da garin sabulu ba ya jawo hankulan kasashen duniya. Nan gaba kadan zai bauta wa masu kashe kudi na kasashen waje.(Tasallah)


1  2