Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-17 17:22:26    
Injin wanke tufafi da ke aiki ba tare da yin amfani da garin sabulu ba

cri

Yanzu lokaci ya yi da za mu gabatar muku da shirinmu na kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya. A cikin shirinmi na yau, za mu karanta muku wani bayani da wakilin gidan Rediyon kasar Sin ya taho da shi, bayan da ya ziyaraci wata kasuwar kayayyaki masu aiki da lantarki . Kan bayanin nan shi ne 'injin wanke tufafi da ke aiki ba tare da yin amfani da garin sabulu ba'.

A cikin wata kasuwar kayayyaki masu aiki da lantarki, wakilinmu ya ji mamaki sosai, a lokacin da masu sayarwa suke nuna yadda injin wanke tufafi da ke aiki ba tare da yin amfani da garin sabulu ba yake aiki.

Mai sayarwa ya ajiye wani tawul da cike yake da binegar da miya da lemo da irin wadannan abubuwa maras tsabta a cikin wannan injin wanke tufafi na musamman, kafin wannan kuma, an riga an cika wannan inji da ruwa, daga baya, injin ya fara aiki, bayan 'yan mintoci da dama, ya tsabtaci tawul din nan sosai. Donme injin nan ya iya tsabtaci tufafi ba tare da yin amfani da garin sabulu ba? Wakilinmu ya yi tambaya ga Mr. Lv Peishi, darektan sashen binciken injunan wanke tufafi na kamfanin Haier. Mr. Lv ya bayyana cewa,

'wannan injin wanke tufafi yana sha bamaban da sauran injunan wanke tufafi daga fannoni daban daban. Muhimmin abu na wannan inji shi ne wani baho na lantarki, wato electrolytic bath a turance, wanda ya iya tsabtaci tufafi sosai ba tare da yin amfani da garin sabulu ba.'

Kamfanin Haier ya samar da wannan injin wanke tufafi ba tare da yin amfani da garin sabulu ba ne don kiwon lafiyar mutane da kiyaye muhalli. Kamfanin Haier ya kafa wata sabuwar kungiyar da ke kunshe da sassan raya kasuwa da nazari da ba da ayyukan hidima bayan sayarwa da harkokin 'yancin mallakar ilmi da sauran sassa 4, dukan masu nazari sun yi shekaru 4 suna yin kokari, a karshe dai, sun samar da injin wanke tufafi da ke aiki ba tare da yin amfani da garin sabulu ba. Bisa sakamakon da cibiyar dudduba da sa ido kan ingancin kayayyaki masu aiki da wutar lantarki ta kasar Sin ta bayar, an ce, kwarewar wannan inji a fannin wanke tufafi ta karu da kashi 25 cikin dari, in an kwatanta shi da sauran injunan wanke tufafi da suke aiki da garin sabulu.


1  2