Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-14 19:02:50    
An bude dandalin tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin gabobi biyu na Zirin Taiwan a nan Beijing

cri

Tsohon shugaban Jam'iyyar Kuomintang wato Lien Chan shi ma ya ba da lacca a gun dandalin tattaunawar, inda ya bayyana, cewa bisa yanayin yanzu na bunkasa tattalin arzikin duniya bai daya, kamata ya yi a yi hadin gwiwa tsakanin shiyya-shiyya ; Sa'annan Lien Chan ya yi kira ga hukumar Taiwan da ta daidaita maganganu bisa matsayin hakika, wato ke nan ta hada fifikon da yankin Taiwan da yake da shi a fannin kudu, da fasaha da kuma na kwararrun mutane da bunkasuwar tattalin arzikin babban yankin kasar. Lien Chan ya fada cewa :'A shekarar 2000, Jam'iyyar Demokuradiyya da Ci gaba ta hau kan kujerar mulki, wadda kuma ta kawo cikas ga bukatun yalwatuwar tattalin arzikin yankin Taiwan sakamakon matsayin siyasa da jam'iyyar din ta dora masa. Daidai bisa irin wannan yanayi ne, 'yan-uwa na Taiwan suka bude babbar kofa yayin da suka yi watsi da hukumar Taiwan domin yin musanye-musanye a fannin tattalin arziki da cinikayya tsakanin gabobi biyu.'

Bugu da kari kuma Lien Chan ya jaddada, cewa kokarin da jam'iyyar Kuomintang da Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin suke yi tare, ya riga ya samar da wata kyakkyawar dama ga gabobin biyu a fannin hadin gwiwa da taimakon juna.

Manyan jami'ai na jam'iyyun nan biyu, da shugabannin kamfanoni da masana'antun kasuwanci da abun ya shafa na gabobi biyu da kuma wassu kwararru da masana a fannin tattalin arziki da yawansu ya zarce 500 sun halarci dandalin tattaunawar. ( Sani Wang )


1  2