Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-14 19:02:50    
An bude dandalin tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin gabobi biyu na Zirin Taiwan a nan Beijing

cri

Yau Juma'a, a nan Beijing, an yi bikin bude dandalin tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin gabobi biyu na Zirin Taiwan a nan Beijing. Manyan jami'ai na Jam'iyyar Kuomintang da na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin mahalartan dandalin sun bayyana,cewa ya kasance da boyayyen karfi a fannin hadin gwiwar tattalin arziki dake tsakanin gabobi biyu ; Wajibi ne 'yan uwa na gabobi biyu su yi amfani da wannan kyakkyawar dama, su kara hadin kansu, su dinga habaka moriya da sukan samu da juna da kuma sanya kokari wajen tabbatar da samun riba mai tsoka tsakaninsu.

Shirya dandalin tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin gabobi biyu na Zirin Taiwan, ya zama daya daga cikin ra'ayoyin da suka tashi daya, wadanda babban sakatare Hu Jintao na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da tsohon shugaban Jam'iyyar Kuomintang suka samu a watan Afrilu na shekarar bara. A gun dandalin tattaunawar, za a yi nazari da shawarwari kan batutuwa guda biyar, wato batun tasiri mai yakini da musanye-musanyen tattalin arziki da cinikayya tsakanin gabobi biyu zai jawo wa tattalin arzikin gabobin biyu, da hadin gwiwa a fannin sha'anin noma, da zirga-zirga kai tsaye, da yawon shakatawa da kuma na sha'anin kudi.

Mr. Jia Qinglin, mamban din-din-din na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam' iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta duk kasar ya ba da lacca a gun tattaunawar, inda ya fito da shawarwari guda hudu a game da yadda za a kara yin musanye-musanye da hadin gwiwa tsakanin gabobin biyu a fannin tattalin arziki. Mr. Jia Qinglin ya ce :' Shawara ta farko ita ce, a mayar da aikin kawo zaman jin dadi ga jama'a a gaban komai don tabbatar da samun bunkasuwa da wadatuwa na gabobi biyu tare ; Ta biyu ita ce, a kago sabon halin yalwata dangantakar dake tsakanin gabobi biyu a fannin tattalin arziki kamar yadda ya kamata ; Shawara ta uku ita ce, a mai da hankali sosai kan daga matsayin fasaha da na takara don ingiza dangantakar dake tsakanin gabobi biyu a fannin tattalin arziki lami-lafiya ; Shawara ta hudu wato ta karshe ita ce, a tattara karfi da kara nuna hikima don ingiza hadin gwiwa da samun moriya da juna tsakanin gabobi biyu ta hanyar kara yin musanye-musanye'.

1  2