Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-14 15:26:44    
An shirya gagarumar gasar gudun dogon zango wato Marathon a Xiamen na kasar Sin

cri

Wani halin musamman na gasar Marathon da akan yi a Xiamen, shi ne har kullum 'yan-uwa na yankin Taiwan sukan mayar da martani mai yakini ga halartar wannan gasa. Mr. Wu Jingguo, mamban kwamitin wasannin Olympics na duniya kuma shugaban kwamitin wasannin Olympics na Taipei yakan ja ragamar kungiyar wasa zuwa Xiamen don halartar gasar Marathon da akan yi a kowace shekara. Ya fada wa manema labaru, cewa :'Dimbin mutane sukan samu kudin yabo da yawa idan sun ci nasara wajen shiga gasar Marathon ta Xiamen wadda matsayinta sai kara daguwa yake a kowace rana. Gasar Dogon zango ta Marathon, gasa ce ta jama'a. Don haka, ina fatan mutane masu yawa na yankin Taiwan za su iya fafatawa a wannan gasa '.

A wannan shekara, kwamitin kula da harkokin shirya gasar gudun dogon zango wato Marathon ta kasa da kasa ta Xiamen da kwamitin kula da harkokin shirya gasar gudun dogon zango ta Taipei sun kuma rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa don kara yin musanye-musanye da yin koyi da juna.

Mataimakin shugaban hukumar kula da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin Mr. Wang Dawei ya fadi, cewa:'Lallai gasar gudun dogon zango wato Marathon da a kan yi a kowace shekara a Xiamen ta yi kunnen doki da irin wannan gasa da akan yi a yanayin kaka na kowace shekara a Beijing. Lamarin gasar Maratho na Xiamen ya shahara ne saboda gwamnati da jama'ar wannan birni sun nuna himma da kwazo wajen shirya da kuma shiga gasar.

Ko shakka babu, wani irin kyakkyawan sakamako da jama'ar birnin Xiamen suka samu wajen shirya irin wannan gagarumar gasa, shi ne sun samu damar gwada fuskar ni'imtaccen wuri da kuma kyakkyawar zamantakewar al'adu na Xiamen ga mutane a kan hanyar yin gudun dogon zango na Xiamen.( Sani Wang )


1  2