Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-14 15:26:44    
An shirya gagarumar gasar gudun dogon zango wato Marathon a Xiamen na kasar Sin

cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba, an samu nasarar shirya wata gagarumar gasar gudun dogon zango wato Marathon a birnin Xiamen na lardin Fujian na kasar Sin. Lallai an samu babban ci gaba wajen shirya irin wannan gasa ta duniya kodayake an soma yinta ne a shekarar 2003. Yanzu ana iya fadin cewar gasar dogon zango wato Marathon ta riga ta shiga sahun gaba wajen shirya gagaruman gasanni da akan yi a duniya.

Birnin Xiamen yana cikin lardin Fujian dake kudancin kasar Sin, wanda kuma yake kusa da yankin Taiwan. Lallai yanayin wurin uyana da kyau, wanda kuma yake dacewa da yin gudun dogon zango. Shekarar bana, shekara ce ta 4 da aka yi wannan gasa. Domin ba da tabbaci ga yin wannan gasa da kyau, an fito da kyawawan shirye-shirye a fannin jiyya, da zirga-zirga da kuma na yin hidima da dai sauransu. Ban da wannan kuma, kwamitin kula da harkokin shirya gasar gudun dogon zango na Xiamen yakan gayyaci wassu nagartattun 'yan wasa na gida da na waje a kowace shekara don shiga gasar. ' Yan wasa Chebunei Munji da Raymond Kipkoech daga kasar Kenya sun zo nan birnin Xiamen don gasar Marathon da aka yi a wannan shekara. Mr.Munji ya fadi, cewa' Ina farin ciki matuka da halartar wannan gagarumar gasa. Ina son Xiamen kwarai domin mutanen wannan birni suna da zafin nama kuma suna son baki ainun'.

1  2