Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-13 18:53:07    
Da farko ne gwamnatin kasar Sin ta shirya taron duniya na addinin Buddha

cri

Kasashen duniya ma sun mai da hankali kuma sun nuna fatan alheri ga wannan dandali. A cikin sakonsa na taya murnar kafuwar dandalin, Kofi Annan, babban sakataren M.D.D. ya yaba wa addinin Buddha cewar addinin Buddha yana yada tunanin nuna soyayya da tausayi da fahimta da girmamawa. Bugu da kari kuma, Mr. Annan ya ce, tunanin zaman lafiya da addinin Buddha yake bi ya riga ya samu amincewa daga jama'a a kai a kai. Kamar yadda addinin Buddha yake yi, tunani mai zaman jituwa wani muhimmin tunani ne na al'adun kasar Sin. Kasar Sin tana yada irin wannan tunani kuma ta ba da shawarar kafa wata duniya mai zaman jituwa inda ake tabbatar da zaman lafiya da neman bunkasuwa tare.

Bugu da kari kuma, kasar Sin tana bin manufar bin addini cikin 'yanci. Tsarin mulkin kasar Sin da sauran dokoki duk suna kare ikon bin addini na jama'a. Yanzu a nan babban yankin kasar Sin kawai, akwai mutane kusan miliyan dari 1 suke bin addinin Buddha tare da dakunan ibada na addinin Buddha fiye da dubu 20. Masu bin addinin Buddha wadanda suke halartar taron dandalin kuma suka zo daga kasashen waje sun yaba wa manufar bin addini cikin 'yanci da gwamnatin kasar Sin take dauka. Mahinda Sangharaerhita, wani babban limamin addinin Buddha daga kasar Sri Lanka ya ce, "Kasar Sin tana bin manufar 'yancin bin addini. Jama'arta suna da ikon zaben addinin da suke son bi. Shirya wannan dandali ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana da ladabi sosai ga addinai iri iri. Wannan ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana girmama ra'ayoyin jama'a." (Sanusi Chen)


1  2