Jama'a masu karatu, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Mu Leka kasar Sin. A ran 13 ga wata, an fara taron dandalin duniya na fadin albarkacin bakinka kan addinin Buddha a birnin Hangzhou, wato hedkwatar lardin Zhejiang da ke kudu maso gabashin kasar Sin. Wannan ne karo na farko da gwamnatin kasar Sin ta shirya irin wannan taron duniya na addini. Masu bin addinin Buddha kusan dubu 1 da mutane wadanda suke nazarin addinin Buddha da jami''ai wadanda suka zo daga kasashe da yankuna fiye da 30 sun halarci wannan taro. Babban taken wannan taro shi ne "Kafa wata al'umma mai zaman jituwa daga zuciya" domin kafa wani dandalin koli na tattaunawa don 'yan Buddha. Yanzu ga wani bayanin musamman da wakiliyarmu ta aiko mana daga birnin Hangzhou.
A karnin 6 zuwa karnin 5 kafnin haihuwar Annabi Isa A.S ne, addinin Buddha ya bulla a kasar Indiya. Yau da shekaru fiye da dubu 2 da suka wuce, an shigo da addinin Buddha a nan kasar Sin, an kuma hada shi da al'adun gargajiya na kasar Sin. Yanzu addinin Buddha ya riga ya zama daya daga cikin muhimman addinan da ke kasancewa a nan kasar Sin. Lokacin da yake bayar da wani jawabi a gun bikin kaddamar da taron, limamin limamai na addinin Buddha Sheng Hui, mataimakin babban sakataren ofishin shirya taron dandalin fadin albarkacin bakinka, kuma zaunannen mataimakin shugaban kungiyar addinin Buddha ta kasar Sin ya bayyana cewa, kafa dandalin fadin albarkacin bakinka na duniya ya bayyana ra'ayi daya na 'yan Buddha na duk fadin duniya. Limamin limamai na addinin Buddha Sheng Hui ya ce, "Dalilin da ya sa aka kafa dandalin fadin albarkacin bakinka kan addinin Buddha shi ne kafa wani dandali don dukkan 'yan Buddha na-gari wadanda suke kishin duniya da mai da hankali kan jama'a da kare addinin Buddha tare da tausayi da soyayya. Za a bi manufar nuna soyayya da tausayi, wayin kai, daidaito da nuna sassauci domin tattaunawa kan maganganun da suke jawo hankulan mutane. Sannan kuma za a yada tunanin addinin Buddha domin kwantar da hankulan mutane da kafa wata al'umma mai zaman jituwa da kuma tabbatar da zaman lafiya da fatan alheri ga dan Adam."
1 2
|