Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-10 18:29:20    
Asibiti na Songtang na Beijing

cri

Saboda mutanen da aka kwantar da su cikin asibiti na Songtang tsofaffi ne kuma suna bakin mutuwa, shi ya sa tun da aka kafa shi, asibitin nan ta tsara tsarin kula da lafiyar majiyyata daga duk fannoni da zaman rayuwarsu cikin sa'o'i 24. Likitoci da nas-nas sun yi ayyukansu a duk sa'o'i 24; sa'an nan kuma, akwai wani ma'aikaci da ke kula da majiyyata a cikin ko wane daki, wanda ya yi zaman rayuwa tare da majiyyata a duk sa'o'i 24.

Ban da wannan kuma, asibiti na Songtang na da wani halin musamman daban, wato ya zuwa yanzu jami'o'i da hukumomin da ba na gwamnati ba fiye da 200 sun kulla hulda a tsakaninsu da asibiti na Sontang cikin dogon lokaci, masu aikin sa kai su kan je dakunan majiyyata a lokacin huta, sun nuna musu wasan kwaikwayo, su yi hira da su, su kula da su. A ganin masu aikin sa kai, suna jin dadi sosai saboda ayyukan da suka yi sun ba da taimako wajen kawar da wahalolin da majiyyatan suke sha a yayin da suke bakin mutuwa.

A cikin wannan asibiti, mun gamu da wata tsohuwa, madam Li mai shekaru 91 da haihuwa, wadda ke fama da ciwon kansa. Ta ce, "na dade ina zama a nan, a ganina, asibiti na Songtang gidana ne, yanzu ni wata mamba ce ta asibiti na Songtang, ina jin dadin zamar rayuwata a nan."

Madam Li tana hira tana murmushi, ba a gane cewa, tana fama da ciwon kansa ba, a fuskarta. A cikin wannan asibiti, dukan mutane su kan yi murmushi.

(??)

Yanzu akwai tsofaffi fiye da miliyan 130 a kasar Sin, yawansu ya kai kashi 10 cikin dari bisa dukan mutanen kasar. Yadda aka kula da su, musamman ma wadanda suke fama da cututtuka masu tsanani, suke bakin mutuwa ya jawo hankulan rukunnoni daban daban na kasar Sin.

A halin da ake ciki yanzu, ya kasance da hukumomin kula da mutanen da ke bakin mutuwa fiye da 100 kamar asibiti na Songtang a kasar Sin gaba daya, inda ma'aikata dubai suke aiki a can, a wasu jami'o'in kasar kuma, an samar da darussa game da kula da mutanen da ke bakin mutuwa; ban da wannan kuma, kasar Sin ta yi shirin kafa hadaddiyar kungiyar aikin kula da mutanen da ke bakin mutuwa, tana fata zaman al'ummar kasar zai kara himmantuwa ga kan wannan aiki.

To, masu sauraronmu, wannan shi ya kawo karshen shirin 'kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya' daga nan sashen Hausa na Rediyon na Kasar Sin, *** ne ke cewa ku huta lafiya.


1  2