Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-10 18:29:20    
Asibiti na Songtang na Beijing

cri

Asibiti na Songtang na Beijing wani asibiti ne da ake kwantar da majiyyata da suke fama da cututtuka masu tsanani, suke bakin mutuwa. Ana kula da su sosai a karshen rayuwarsu, ta yadda za su manta da ciwo da kuma barazanar mutuwa, suna iya riga mu gidan gaskiya cikin mutunci.

Bayan da muka shiga wannan asibiti, muna shakkar cewa, ko wannan wani asibiti ne ko kuma wani wurin shakatawa ne. A tsakiyar fargagiyarsa, tsofaffi fiye da 10 suna zaune tare, wasu suna rera waka, wasu suna motsa jiki, amma dukansu suna fama da cututtuka.

Asibiti na Songtang, mai shekaru misalin 20, wani asibiti ne na musamman da ke karbar majiyyatan da aka tabbatar da cewa, ba za a iya warkar da su ba, tana kula da su daga duk fannoni, tana sassauta tashin hankali da rashin jin dadi da ke cikin zukatansu, sa'an nan kuma, tana kula da majiyyata dare da rana. Akwai dakuna misalin dari da kuma ma'aikatan kiwon lafiya fiye da dari a cikin asibiti na Songtang, majiyyata fiye da 230 suna zama a nana a yanzu, yawancinsu tsofaffinsu.

Shugaban asibitin Mr. Li Wei yana ganin cewa, ko da yake Sinawa suna nuna girmamawa da kulawa ga tsofaffi bisa al'adun gargajiyarsu, suna kula da tsofaffi sosai a fuskar zaman rayuwa, amma majiyyatan da suke bakin mutuwa ba kawai suna bukatar kulawa a fuskar zaman rayuwa ne ba, shi ya sa asibitoci kamar asibiti na Songtang suke da matukar muhimmanci, ya ce, "tsofaffin da suke bakin mutuwa suna da bukatu iri daban daban, ban da taimako da suke samu daga 'ya 'yansu kawai. A bayyane ne iyalai ba su iya biyan dukan bukatun majiyyata ba, saboda su ba likitoci ba ne. Idan suna son girmama da kula da iyayensu, to, kada su ki karbar kulawa daga dukan zaman al'ummar kasar, sun iya yin la'akari da asibitinmu. "

1  2