Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-10 18:10:39    
New Zealand kasa ce mai ni'ima da ke tsibiri

cri

Tun bayan da kasar Sin da New Zealand suka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu a ran 22 ga watan Disamba na shekara ta 1972, an yi ta yalwata huldar aminci da ke tsakaninsu. A cikin 'yan shekarun nan, huldar tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin bangarorin biyu tana bunkasa da sauri. A halin yanzu dai, kasar Sin tana daya daga cikin abokan ciniki mafiya muhimmanci na kasar New Zealand. A shekara ta 2005, yawan cinikin da aka yi tsakanin kasashen biyu ya kai dallar Amurka biliyan 2.68. New Zealand ita kuma kasa ce mai ci gaba ta farko da ta amince da cikakken matsayin tattalin arzikin kasar Sin na kasuwanni, haka kuma kasa ce mai sukuni ta farko da ta yi shawarwari tare da kasar Sin a kan kulla huldar ciniki mai 'yanci tsakanin bangarorin biyu.(Lubabatu Lei)


1  2