Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-10 18:10:39    
New Zealand kasa ce mai ni'ima da ke tsibiri

cri

Kasar New Zealand tana kudu maso yammacin tekun Pasifik, kuma tana hangen kasar Australia ta tekun Tasman. Kasa ta New Zealand ta hada da tsibirin kudu da na arewa da kuma wasu kananan tsibirai. Yawan fadin kasar ya kai muraba'in kilomita sama da dubu 270. Wellington, hedkwatar kasar, babban birni ne da ya fi kasancewa a kudu a duk duniya.

Kasar New Zealand tana da mutanen da yawansu ya kai miliyan 4 da dubu 70, wadanda kashi 78.8% daga cikinsu zuriyoyi ne na 'yan kaka gida daga Turai, kuma mutanen Maori sun dau kashi 14.5% daga cikinsu, a yayin da yawan 'yan asalin Asiya ya kai kashi 6.7%. Mazaunan kasar da yawansu ya kai kashi 70% suna bin addinin Krista ko kuma Katolika. Turanci da harshen Maori harsuna ne da ake amfani da su a wajen gudanar da ayyuka a kasar.

A karni na 14, mutanen Maori sun je New Zealand kuma sun fara zama kasar. Ya zuwa karni na 18, bakin kasar Birtaniya masu dimbin yawa sun kaura zuwa kasar, kuma Birtaniya yi shelar mamaye kasar. A shekara ta 1840, New Zealand ta zama kasar da ke karkashin mulkin mallakar Birtaniya. A shekara ta 1947, New Zealand ta sami mulkin kanta, kuma ta zama 'yar kungiyar commonwealth.

New Zealand ta shahara ne sabo da muhallinta mai kyau. A kasar, akwai duwatsu da tuddai masu yawa wadanda suka dau sama da kashi 75% na fadin kasar. A kasar, ba a samun bambancin yanayi sosai ba a duk shekara, kuma akwai bishiyoyi masu yawa wadanda ke fadin filin da ya kai kashi 29% na fadin kasar. Ban da wannan, yawan makiyaya na kasar ya kai rabin fadin kasar. Bishiyoyi da makiyaya masu yawa sun sa New Zealand ta zama wata kasa mai launin kore shar a zahiri. Idan an hangi New Zealand daga sararin sama, sai ka ce dutse ne kore da ke cikin tekun Pasifik.

New Zealand ta kasaita sabo da tattalin arzikinta. Aikin kiwon dabbobi shi ne tushen tattalin arzikinta. Kayayyakin dabbobi sun kai kashi 50% daga cikin dukan kayayyakin da take fitarwa zuwa kasashen waje. Yawan naman rago da kayayyakin madara da kuma gashin tumaki da take fitarwa zuwa kasashen waje ya zo na farko a duk duniya. Bayan haka kuma, New Zealand ta kuma wadata da kifaye iri iri.

Kasar New Zealand tana da kyakkyawan muhalli da kuma yanayi mai kyau. Wuraren yawon shakatawa sun barbazu a ko ina a kasar. Tsibirin arewa na kasar yana da dimbin duwatsu masu aman wuta da kuma idanuwan ruwa masu zafi. A tsibiri na kudu kuma, akwai kogunan kankara da tafkuna da yawa. Musamman ma a tsibirin arewa, dutse mai aman wuta din nan na Ruapehu tare da duwatsu masu aman wuta 14 da ke kewayensa sun kasance yanayin musamman na duniya. A wurin kuma, akwai idanuwan ruwa masu zafin gaske sama da 1,000, wadannan idanuwan ruwa iri daban daban sun zama wurare masu ban mamaki na kasar. A halin yanzu dai, yawan kudin da ake samu daga aikin yawon shakatawa na kasar ya kai kashi 10% daga cikin yawan GDP nata, wanda kuma ya zo na biyu, wato bayan masana'antar kayayyakin madara a wajen samun kudin shiga na kasar. A shekara ta 2004, mutanen waje da suka je kasar New Zealand don yawon shakatawa sun kai miliyan 2 da dubu 350.

1  2