Ya kuma ce, babbar ganuwar dake kasancewa a wuraren dake arewacin kasar Sin da aka gina ne a karni na 7 na kafin bayyanuwar "Annabi Isa",Amma bayan haka cikin shekaru fiye da dubu biyu da suka shige, sarakuna na dauloli daban daban sun yi dinga yin gyare gyare da kyautata babbar ganuwar da aka gina. Daga karni na l4 zuwa karni na l7 na bayyanuwar Innabi Isa, an gina babbar ganuwar dake birnin Beijing, wato daga wurin bakin teku na gabashin kasar Sin zuwa wuraren yammacin dake kusa da Hamada.
Wani babban sakatare na kungiyar masu ilmin babbar ganuwa na kasar Sin Mr.Dong Yaohui yana gana cewa, yanzu an fara aikin yin safiyo ga babbar ganuwa yana da babbar ma'ana, ya kuma gaya wa wakilin rediyonmu cewa, aikin yin safiyo ga babbar ganuwar dake kasancewa cikin birnin Beijing yana da muhimmanci sosai, domin a daular Min an fara gina wannan babbar ganuwa mai karfi sosai.Daga shekarar nan da muke ciki ne gwamnati ta fara yin aikin kiyaye babbar ganuwa. An yi kimanta cewa, in za a kammala wannan babban aikin yin safiyo har cikin shekaru l0 masu zuwa, domin wannan aikin yana shafe sassa daban daban, misali za a yi safiyo da kafa dakin ajiye abubuwan da aka rubuta da tsara dabarun kiyaye da kafa tsarin kulawa da dai sauransu.
Wannan babban sakatare ya ce, kullum akwai labarun da sassan watsa labaru suka bayar game da wadansu mutane sun lahanta babbar ganuwa, har yanzu ba a yanke hukunci ga masu kawo barna ga babbar ganuwa, domin har yanzu ba a kafa tsarin dokokin kiyaye babbar ganuwa ba tukuna, sabo da haka ne ya kamata da farko za a kafa tsarin dokokin kiyaye babbar ganuwa bisa doka, wato in za a lahanta babbar ganuwa za a yi iya yanke masa hukunci bisa shari'a.
Yanzu an kuma hana yin gine gine a wuraren dake kewayen babbar ganuwa, kuma dole ne za a rushe dukkan gine ginen da aka yi a wuraren dake kusa da babbar ganuwa.(Dije) 1 2
|