Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-10 10:48:22    
Kasar Sin ta fara yin aikin kiyaye babbar ganuwa

cri

Har kullum ne jama'ar kasar Sin suna sa muhimmanci kan kiyaye babbar ganuwa domin ita ce kayan tarihi na al'adun 'yan adam. Amma har yanzu dai an kasance da matsalar game da tsawon babbar ganuwar dake kasancewa a kasar Sin. Yanzu, wani sashen da abin ya shafa yana yin share fage don fara yin safiyo kan dukkan babbar ganuwa dake kasancewa bisa babban mataki. Yanzu ga abubuwan da wakilin rediyon kasar Sin ya rubuto mana filla filla; daga karkarar birnin Beijing da wuraren dake kewayen birnin Beijing, an kasance da babbar ganuwar tarihi a wurare daban daban. Amma yawacin masu shakkatawa na gida da na kasashen waje sukan kai ziyara a babbar ganuwar dake birnin Beijing. Kuma wani sashen kula da kiyaye babbar ganuwa na kasar Sin shi ma ya fara yin safiyo daga nan birnin Beijing.

Yanzu, bayan da aka yi horo ga wadansu masu aiki wajen koyon ilmin yin safiyo, sai sun fara yin safiyo ga dukkan tsawon babbar ganuwar dake kasancewa a wurare daban daban.

Shugaban ofishin kula da kiyaye kayayyakin tarihi na birnin Beijing ya gaya wa wakilin rediyonmu cewa, Cikin 'yan shekaru da suka shige, mun riga mun fara yin gyare gyare da kyautata babbar ganuwa bisa babban mataki. A shekarar nan da muke ciki, jimlar kudin da za mu zuba kan aikin kiyaye babbar ganuwa za su kai kudin Sin yuan wajen miliyan 20 zuwa 30.

1  2