Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-07 15:31:05    
Bari mu dudduba tuffafin alama masu suna na kasashen duniya

cri

Mr. Wu Yan wanda ke kula da aikin fama da Pyramid Selling a babbar hukumar sa ido kan odar kasuwanni da masana'antu ta kasar Sin ya bayyana cewa, "Hanyar Pyramid Selling ta haddasa matsaloli da yawa a nan kasar Sin. Bayan da majalisar gudanarwa ta gwamnatin kasar Sin ta bayar da sanarwar hana yin amfani da hanyar Pyramid Selling a nan kasar Sin, hukumomin sa ido kan odar kasuwanni da masana'antu da hukumomin tabbatar da zaman karkon jama'a na wurare daban-dabam na kasar Sin suna fama da irin wannan hanya."

A cikin 'yan shekarun nan, Sinawa sun fi son sayen kayayyaki da masana'antu suke sayar kai tsaye. A sa'i daya, lokacin da shigowar kasar Sin a cikin kungiyar WTO, kasar Sin ta taba bayyana cewa, dole ne a karshen shekara ta 2005, za ta yarda da a yi dillancin kayayyaki kai tsaye a kasar Sin. A sakamakon haka, hukumomin da abin ya shafa sun bayar da Takardar Sa Ido kan Dillancin Kayayyaki Kai Tsaye da Takardar Hana Sayar da Kayayyaki ta hannu hannu, wato Pyramid Selling.

A cikin wadannan takardu, an tabbatar da ma'anar hanyar dillancin kayayyaki kai tsaye da ma'aunonin yin wannan aiki ga masana'antu da mutane wadanda suke son yin wannan aiki.

Mr. Yang Qian wanda ke yin nazari kan hanyar dillancin kayayyaki kai tsaye ya bayyana cewa, "Bayan da aka bayar da wadannan takardu biyu, masana'antu da mutane suna da ma'aunonin yin wannan aiki. A da, ba mu iya tabbatar da cewa ko wace masana'anta ta bin hanyar dillancin kayayyaki kai tsaye, ko kuma wace masana'anta ce ke sayar da kayayyakinta ba ta hanyar halal ba."

Bugu da kari kuma, a cikin wadannan takardu biyu, an tsara ka'idojin cewa, mutane wadanda ba su kai shekaru 18 da haihuwa ba da dalibai da malamai da likitoci da sojoji da ma'aikatan da ke aiki a masana'antun da ke dillancin kayayyaki kai tsaye da mutanen kasashen waje ba za su iya yin wannan aiki ba. Sannan kuma, mutane wadanda suke son yin wannan aiki dole ne su nemi takardar samun izinin yin wannan aiki.

Mr. Liu Xin wanda ya taba yin aikin daukar murya a wani gidan rediyo, yanzu ya yi murabus daga wannan gidan rediyo ya fara yin aikin dillancin kayayyaki kai tsaye. Mr. Liu ya ce, "A ganina, hanyar dillancin kayayyaki tana dacewa da halin da ake ciki yanzu. Za a iya samun kudi, amma bai kamata a bayyana cewa, za ka iya zama mai arziki a cikin kwana daya kawai ba. Wannan wani aiki ne kawai."


1  2