Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-03 17:14:47    
Me ya sa ministan harkokin waje na Britaniya da Amurka suka yi ziyara a Iraki ba zato ba tsammani?

cri

Manazarta suna ganin cewa, na daya, kasashen biyu suna neman mayar da kasar Iraki da ta zama alamar ci gaba ga babban daftarinsu na gabas ta tsakiya, ta yadda za su sake kafa tsarin dokoki a gabas ta tsakiya ta hanyar yadada irin dimokuradiyyarsu. Amma idan yakin basasa ya barke a kasar Iraki, halin da ake ciki ya kara yamutsewa, hargitsi da ake yi a tsakanin rukunomin musulmi ya game duk yankin gabas ta tsakiya, to, misalin dimkokuradiyya irin na Amurka a gabas ta tsakiya kamar Iraki zai zama abin dariya.

Na biyu, gwamnatocin kasashen Amurka da Britaniya sun gamu da matsi mai zafi daga wajen gamayyar kasa da kasa domin yakin Iraki da suka tayar, kuma sun kasa samun goyon baya daga wajen masu zabe da yawa a gida. Amma shugabannin kasashen biyu sun yi ta kare manufofinsu game da harkokin Iraki bisa sanadiyyar surutun baki na wai kawo wa jama'ar kasar Dimokuradiyya. A sakamakon tabarbarewa halin da ake ciki a kasar Iraki, hargitsi da ake yi da karfin tuwo ya kara zafi, mutane da ke mutuwa da jin raunuka sun karu, sai a yi tambaya cewa, idan ba a iya tabbatar da zaman alfiya ga jama'ar Iraki, to, yaya za a yi magana kan dimokuradiyya?

Na uku, ko da yake an riga an kawo karshen yakin Iraki da kasashen Amurka da Britaniya suka tayar a cikin shekaru 3 da suka wuce, yanzu da kyar kasashen biyu za su yi hakuri da halin da ake ciki game da barkewar yakin basasa a Iraki.

Daga bisani, yawan sojojin kasar Amurka da ke girke a kasar Iraki ya kai dubu 133 a yanzu, hukumar sojoji ta kasar Amurka tana so za ta rage sojojinta zuwa dubu 100 kafin karshen shekarar nan, haka nan kuma kasar Britaniya ita ma ta bayyana a kwanan baya ba da dadewa ba cewa, za ta janye jikin sojojinta 800 daga cikin 8500 a watan gobe. Amma babban sharadinsu na janye sojoji shi ne sai rundunar 'yan sanda ta kasar Iraki sun iya daukar nauyin da ke bisa wuyansu na kare zaman alfiya. Idan yakin basasa ya barke a kasar Iraki, to, mai yiwuwa ne, da kyar za su gudanar da shirinsu na janye sojoji, burin sojoji na komawa gida ma zai bi ruwa.(Halilu)


1  2