Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-03 17:14:47    
Me ya sa ministan harkokin waje na Britaniya da Amurka suka yi ziyara a Iraki ba zato ba tsammani?

cri

Ran 2 ga wata, Jack Straw, sakataren harkokin waje na kasar Britaniya da takwararsa Condoleezza Rice ta kasar Amurka sun yi ziyara a birnin Bagadaza, hedkwatar kasar Iraki ba zato ba tsammani, inda suka yi tattaunawa a tsakaninsu da shugabannin bangarori daban daban da abin ya sata na kasar Iraki a kan batun kafa gwamnatin hadin guiwa ta kasar tun da wuri.

Kafofin watsa labaru suna ganin cewa, ziyarar da ministocin nan biyu suka yi tare a wannan gami, ta bayyana babbar damuwa da kasashen Britaniya da Amurka ke nunawa ga rashin kafa sabuwar gwamnatin kasar, makasudin ziyararsu shi ne domin matsa wa bangarorin Iraki lamba.

Daidai ne, bayan da ta gana da shugabannin bangarorin Iraki daban daban, Condoleezza Rice ta bayyana wa manema labaru cewa, ita da Straw sun bayar da labari iri daya ga shugabannin bangarorin nan, wato wajibi ne, ko wanensu ya yi kokari wajen neman kawar da halin kaka-ni-kani da ake ciki tun da wuri don kafa majalisar ministoci. Dalilin da ya sa haka shi ne domin yanzu jama'ar kasar Iraki suna kara kasa hakuri da wannan. Haka nan kuma gamayyar kasa da kasa su ma suna fata za a kafa gwamnatin hadin guiwa ta al'ummar Iraki tun da wuri. Bayan haka Hoshyar Zebari, ministan harkokin waje na kasar Iraki ya tabbatar da cewa, Rice da Straw gaba daya sun karfafa magana a kan aikin kafa gwamnatin hadin guiwa ta al'ummar Iraki da gaggawa. Jinkirtar da aikin nan da aka yi ta yi ya daga Washington da London kwarai.

To, me ya sa kasashen Amurka da Britaniya suke nuna damuwa kamar haka?


1  2