Wannan doka ta tanada cewa, ofishin duba cututtukan dabbobi yana da nauyin duba cututtukan dabbobi bisa wuyansa, in ya samu rahoto kan cututtukan dabbobi masu tsanani ya kamata a aika da mutane zuwa wurin don duba halin da a ke ciki a wajen cututtukan dabbobi, kuma ya yi rahoto ga shugabansa cikin awa biyu. Cikin awa 4 da aka bullo da cututtukan dabbobi, ya kamata gwamnatocin larduna da sassan kula da cututtukan dabbobi su yi rahoto ga majalisar gudanarwa ta kasar Sin.
Wannan doka kuma ta tanada cewa, gwamnatin kasar Sin za ta ba da kyautar maganin rigakafin cututtukan dabbobi a wuraren da a ke yada cututtuka, ban da haka kuma gwamnatin kasar Sin za ta biya diyya ga mutanen da suka yi hasara sabo da an karkashe tsuntsayensu don rigakafin cututtukan tsuntsaye.
A jihar Mongolia ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta a arewacin kasar Sin har yanzu akwai cututtukan annobar murar tsuntsaye. Bayan da aka bayar da Dokar gaggawa game da cututtukan dabbobi masu tsanani, Mr. Wang Junping, mataimakin darektan ofishin ba da umurni ga aikin rigakafin cututtukan tsuntsaye ya zanta da wakilin gidan rediyon kasar Sin cewa, wannan doka tana da muhimmancin gaske a wajen maganin cututtukan tsuntsaye. Ya ce, Wannan doka ta tanada alhakin da ke bisa wuyan gwamnatoci na matakai daban daban a fili. A cikin ayyukanmu na nan gaba, ya kamata mu yi kokarin cika alhakin da ke bisa wuyanmu don maganin cututtukan dabbobi masu tsanani. 1 2
|