Bisa labarin da ma'aikatar sha'anin noma ta kasar Sin ta bayyana, sha'anin ciyar da tsuntsayen gida ya riga ya fito daga inuwar cutar murar tsuntsaye. Kamfannonin da cutar ta shafa sun fara sami moriya.
Yanzu muhimmin lokaci ne ga kasar Sin a wajen rigakafin annobar murar tsuntsaye. To, wadanne matakai ne kasar Sin ta dauka a wajen rigakafin annobar murar tsuntsaye. Kuma wane irin hukunci ne za a yanke wa mutane da sassan gwamnati domin ba su cika alhakin da ke bisa wuyansu ba? Duk wadannan tambayoyi an tanada su a cikin dokar gaggawa game da cututtukan dabbobi masu tsanani da majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta bayar kwanakin baya. A cikin shirinmu na yau, sai ku saurari labarin da wakilin gidan rediyon kasar Sin ya ruwaito mana.
A gun taron bayar da labarum da ma'aikatar noma ta kasar Sin ta shirya jiya, Mr. Yin Chengjie, mataimakin minitan noma na kasar Sin ya bayyana cewa, a wajen rigakafin cututtukan dabbobi masu tsanani kasar Sin ta dauki matakai masu amfani. Dokar gaggawa game da cututtukan dabbobi masu tsanani ta kara kyautata dokokin kasar Sin a wajen rigakafin cututtukan dabbobi masu tsanani. Ya ce, Dokar gaggawa ta rigakafin cututtukan dabbobi masu tsanani ta zama jagora ga kasar Sin a wajen maganin cututtukan dabbobi.
1 2
|