Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-17 18:48:57    
Bankunan kasar Sin suna mai da hankali wajen raya sha'anonin kudi don mutum kadai

cri

Yanzu a nan kasar Sin, ko manyan bankunan kasuwanci na gwamnati ko matsakaita da kananan bankunan kasuwanci na birane, yawancinsu sun bude "dakin sarrafa dukiyoyi" domin mutum kadai, inda suka bayar da hidimomi iri iri, alal misali, sun saya ko sayar da kudin Renminbi bisa rokon bako kuma da makamatansu. Mr. Liang Shuang ya ce, "Alal misali, yanzu wani mutum yana da wasu kudaden da ba zai yi amfani da su a cikin wasu lokuta ba, za mu ba shi shawarar zuba jari a kan wasu asusu, ko sayen inshora da dai sauransu. Muna da irin wadannan hidimomi iri iri."

Yanzu a nan kasar Sin, mutane sun je banki ba ma kawai domin ajiye ko karbi kudi ba, har sun neman izinin zuba jari domin tabbatar da karuwar darajar dukiyoyinsu da kyautata ingancin zamantakewarsu. Mr. Zhao Xijun, shehun malamin hukumar yin nazari kan sha'anin kudi da takardun hannun jari ta jami'ar jama'a ta kasar Sin ya nuna cewa, yanzu yawan kudaden da manyan kamfanonin kudi na kasashen duniya ciki har da Rukunin CitiBank da kamfanin HSBC suka samu domin samara wa mutum hidimar sha'anin kudi ya kai fiye da kashi 40 cikin kashi dari daga cikin dukkan kudaden da suka samu, amma a cikin bankunan kasar Sin, wannan adadi ya kai wajen kashi 10 cikin kashi dari kawai.

Bisa kididdigar da aka yi, adanannun kudaden da jama'ar kasar Sin suka ajiye a cikin bankuna sun riga sun kai kudin Renminbi yuan fiye da biliyan dubu 1 da dari 3. Wadannan kudade sun samar da babbar dama ga yunkurin raya sha'anin kudi na mutum. Amma yanzu, bankunan kasar Sin suna ba da shawarar tafiyar da kudade ga bakinsu kawai. Masana suna ganin cewa, ya kamata bankunan kasar Sin su kara hidimomi iri iri ga bakinsu.

Lokacin da bankunan kasar Sin suke dogara a kansu kuma suke yin kokari wajen raya sha'anin kudi don mutum, suna kuma kokari domin shigowar da tunanin zamani da fasahohin tafiyar da hukumomin sha'anin kudi daga sauran kasashen duniya. A watan Maris na shekara ta 2005, lokacin da bankin gine-gine na kasar Sin ya daddale yarjejeniyar zuba jari bisa manyan tsare-tsare da bankin Amurka, Mr. Guo Shuqing, shugaban bankin gine-gine na kasar Sin ya taba bayyana cewa, wani muhimmin dalilin da ya sa bankin gine-gine na kasar Sin ya yi hadin guiwa da bankin Amurka shi ne kara karfin samar wa mutum hidimar sha'anin kudi. Bankin zirga-zirga na kasar Sin wanda ya rinjaya sauran bankunan kasar Sin wajen shigowar masu zuba jari bisa manyan tsare-tsare, ya riga ya yi ainihin hadin guiwa da bankin HSBC na kasar Ingila. Mr. Liang Shuang, wato direktan ofishin sayar da katunan kudi ga mutum a sashen Beijing na bankin zirga-zirga na kasar Sin ya ce, "A shekara ta 2005, bankin zirga-zirga na kasar Sin ya gama aikin hada kan jarin bankin HSBC. Wannan ya almantar da cewa, bankin zirga-zirga na kasar Sin wanda ya tafiyar da harkokinsa don kamfanoni da masana'antu a da, ya riga ya zama wani bankin da ya fi mai da hankali wajen ba da hidimar sha'anin kudi ga mutum."

A ganin masanan sha'anin kudi, bankunan kasar Sin da na kasashen waje suna yin hadin guiwa ne bisa ka'idar moriyar juna. Bankunan kasar Sin za su iya koyon fasahohi da tunani irin na zamani wajen tafiyar da harkokinsu, bankunan kasashen waje ma za su iya samun fasahohi kan yadda za su iya tafiyar da harkokinsu a nan kasar Sin. Bisa alkawarin da kasar Sin ta dauka lokacin shigowarta cikin WTO, ya zuwa karshen shekara ta 2006, bankunan kasashen waje za su samun izinin tafiyar da harkokin kudin Renminbi a nan kasar Sin. Bankunan kasar Sin da na waje za su yi takara bisa sharadi daya.  (Sanusi Chen)


1  2