Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-17 18:48:57    
Bankunan kasar Sin suna mai da hankali wajen raya sha'anonin kudi don mutum kadai

cri

Mr. Qiao Wei wanda ke aiki a wani kamfanin kula da harkokin yawon shakatawa na Beijing ya kan zuwa kasashen waje. A da, kafin ya tashi daga nan kasar Sin, ya kan sayen wasu kudaden waje ko ya tafi da wasu kudin Renminbi zuwa kasashen waje, sai a kasashen waje ne ya yi musayarsu. Sabo da haka bai ji sauki ba. Domin bisa dokokin kasar Sin da abin ya shafa, bai iya tafiyar da kudade da yawa ba zuwa kasashen waje. Bugu da kari kuma, idan an yi yawon shakatawa tare da kudade da yawa, ba za a ji zaman karko ba. Sakamakon haka, yanzu yana da tunani ko zai iya warware wannan matsala ta banki.

"Domin na fi son yawon shakatawa kuma dalilin aiki, na kan zuwa kasashen waje. Babbar matsalar da ke kasancewa a gabana ita ce ina jin damuwa sosai idan na tafi kasashen waje tare da kudade da yawa. Amma idan na iya yin amfani da katin kudi a kasashen waje, wannan ya fi sauki. Sabo da haka, yanzu ina neman wani katin kudi daga banki."

Kamar bukatar da Mr. Qiao ke nema, yanzu yawancin bankunan jarin kasar Sin fara sayar da katunan kudi iri da za a iya yin amfani da su a kasashen waje. Mr. Liang Shuang, wanda ke kulda aikin sayar da katunan kudi ga mutum a sashen Beijing na bankin zirga-zirga na kasar Sin ya ce, mutane wadanda suke da katin kudin Renminbi da na waje, ba ma kawai za su iya yin amfani da shi a kasar Sin ba, har ma za su iya yin amfani da shi a kasashen waje.


1  2