Wannan mutumin da yake ba da amsa ga wakilinmu shi ne Xu Zhengpeng, wani dan birnin Harbin na lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, lokacin da ingancin zamantakewar jama'ar kasar Sin yake samun kyautatuwa, suna kuma mai da hankula sosai kan muhimman al'amuran siyasa da na tattalin arzikin kasar.
A gun taruruka 2 na shekarar bana, wakilan majalisar dokokin kasar da membobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar za su tattauna shirin tsari na 11 na shekara-shekaru 5 don bunkasa tattalin arziki da jin dadin al'ummar kasar Sin. Mr. Han Meng, wani shehun malami ne na sashen ilmin tattalin arziki na jami'ar yin nazari kan ilmomin zaman al'umma ta kasar Sin, ya bayyana cewa, abin da ya fi kulawa shi ne wannan tsari.
"Na fi kulawa da abubuwan wannan tsari da za a gabatar a filla filla tare da sabuwar hanyar neman bunkasuwar tattalin arziki. Sannan kuma na fi kulawa da yadda za a kyautata tsarin tattalin arziki da raya tattalin arziki kuma da dokokin da za a tsara domin tabbatar da cimma tsarin da ake tsara."
1 2 3
|