Ban da gine-ginen kuma, akwai tsabi'un gargajiya masu ban sha'awa da 'yan birnin Dali ke bi. Alal misali, idan ka sami damar bakutar iyalin 'yan birnin, to, mai gida zai ba ka ruwan shayi iri uku don ka sha. Da farko, za ka sha ruwan shayi mai daci, kana za ka sha ruwan shayi mai zaki, daga baya kuma za ka sha ruwan shayi mai kamshi. Bisa labarin da aka samu daga bakin mutanen zamanin da, an ce, wannan ladabi ne da sarkin kasar Dali na zamanin da ke yi wa gaggan baki. 'Yan birnin Dali sun gaji wannan ladabin ne daga sarkinsu na zamanin da. Da Malama Wang Hongyuan, mai hidima a wani dakin shan ruwan shayi ta tabo magana a kan wannan lababi, sai ta bayyana cewa, "a hakika dai, gaskiya ne a sha irin wadannan ruwan shayi guda uku. Dalilin da ya sa haka shi ne domin sai an sha wahala, a kan ji dadi. Babu yadda za a yi a yi zaman jin dadi, sai an yi kokarin aiki." Haka nan kuma ya kamata, a waiwayi abubuwan da aka yi, kana a gyara kuskure, a yadada halin kirki, ta haka ne za a kara samun sakamako mai kyau. "
Ban da ruwan shayi, za a iya dandana kayayyakin abinci na musamman da 'yan birnin Dali suka shafe shekaru darurruka suna ci. Daga cikin kayayyakin abincinsu, akwai kayan abinci irin na madara da shinkafa da sauransu wadanda suka fi shahara. Bayan da Malama Zhang Qian, 'yar yawon shakatawa ta fito daga birnin Beijing ta ci irin wadannan kayayyakin abinci, sai ta ce, kayayyakin abinci na musamman na birnin Dali akwai iri daban daban, kuma suna da dadin ci ainun.
1 2 3
|